Connect with us

News

Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wasu ’yanbindiga sun yi garkuwa da kimanin yara 12 a Jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya, a wani sabon harin satar mutane da ya faru a yankin kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

Majiyoyin tsaro da mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa maharan sun sace yaran ne ranar Asabar a kusa da garin Maigujeri da ke Ƙaramar Hukumar Rafi, yayin da suke dawowa daga gonar malamin makarantar allo da suke taimakawa wajen girbin masara.

Jami’an NDLEA Sun Kama Wata Mata Da Harsasai 266 Na Bindiga Ƙirar AK-47 A Kan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna ‎

Wani rahoton tsaro da AFP ta gani ya ce an sace yara 18, sai dai wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Abdullahi ya ce adadin yaran da aka sace ya kai kusan 12.

Abdullahi ya ce an harbi ɗaya daga cikin yaran a yayin harin, kuma ana ba shi kulawa a wani asibiti da ke Minna, babban birnin jihar.

Satar yaran na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke ɗauke da manyan makamai, waɗanda aka fi sani da ’yanbindiga, ke ƙara kai hare-hare, yin garkuwa da mutane da satar shanu a sassa daban-daban na Jihar Neja.

Advertisement

Rundunar ’yansandan jihar ba ta mayar da martani ga buƙatar AFP ta neman jin ta bakinta kan lamarin ba.

Wannan sabon hari na zuwa ne bayan wasu jerin hare-haren satar mutane a jihar. A watan Satumba, an yi garkuwa da aƙalla manoma 47, yawancinsu mata, yayin da suke girbin gyada.

Haka kuma, an sace kimanin yara 50 daga wata gona a watan Agusta, waɗanda aka saki daga baya bayan biyan kuɗin fansa.

A watan Nuwambar bara, an sace sama da ɗalibai 250 daga wata makarantar kwana ta Katolika da ke Papiri a Jihar Neja. An saki ɗaliban bayan kusan wata guda, sakamakon biyan kuɗin fansa mai yawa.

 

 

Advertisement

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending