Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka Manyan Shugabannin Daesh A Borno

Published

on

3dda8814 ed59 49ae 94b6 d4b90fb8e0a8 1793559333159
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Sojojin Nijeriya sun kashe wasu ’yanta’addan Daesh da dama, ciki har da wani babban mamba a majalisar Shura ta ƙungiyar da kuma wani fitaccen kwamandanta, yayin wani artabu a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Sojojin sun ce lamarin ya faru ne a ranar 31 ga Oktoban 2026, bayan ’yanta’addan Daesh sun kai wani gagarumin hari kan sansanonin sojojin da ke yankin.

Jami’an NDLEA Sun Kama Wata Mata Da Harsasai 266 Na Bindiga Ƙirar AK-47 A Kan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna ‎

A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana sunayen manyan ’yanta’addan da aka kashe da suka haɗa da Abu Hajara, mamba a majalisar Shura ta ƙungiyar, da Abul Walid, wani kwamanda kuma na kusa da Ba Shuwa, wanda sojojin suka bayyana a matsayin babban jagoran Daesh.

Sojojin sun ce sun yi amfani da dakarun ƙasa da kuma tallafin jiragen yaƙi wajen dakile harin, inda suka ƙwato makamai masu yawa, alburusai da na’urorin sadarwa bayan artabun.

Wannan na zuwa ne ƙasa da kwanaki uku bayan wani samamen soji a Buni Yadi, inda sojojin suka ce sun kashe ’yanta’adda 55, ciki har da wasu manyan kwamandoji da aka bayyana sunayensu da Ali Mandara Abba Gajiri, wanda aka fi sani da Munzir, Habu Ikkima Nakif Yana Faruk da Kwamanda Gogore.

Advertisement

Operation HADIN KAI ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda a yankin, tare da ƙudurin kare fararen hula da kuma lalata sansanonin ’yan ta’addan.

Sai dai ba a samu tabbaci mai zaman kansa kan ikirarin sojojin ba.

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending