News
Jami’an NDLEA Sun Kama Wata Mata Da Harsasai 266 Na Bindiga Ƙirar AK-47 A Kan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun cafke wata mata mai suna Aisha Isah, bisa zargin safarar harsasai 266 na bindigar AK-47 a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
An cafke matar ne a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan hanyar, lokacin da jami’an hukumar ke gudanar da sintiri.
Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Sai dai hukumar ba ta bayyana inda matar ta taho, da inda zata ko kuma yadda ta mallaki harsasan ba. Haka kuma, ba ta yi ƙarin bayani kan ko an miƙa ta ga wata hukumar tsaro domin ci gaba da bincike ba.
Advertisements

