Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yanta’adda 42 A Borno

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Dakarun Operation Hadin kai da ke yaƙi da ‘yanta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yanta’addan aƙalla 42 a hare-haren da suka kai a jihar Borno.

Wata sanarwa da muƙaddashin mai magana da yawun rundunar ta Operation Hadin kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Laraba, ta ce a ranar Litinin 26 ga watan Oktoba, rundunar ta kai samame kan waɗanda ake zargi ‘yanta’adda ne a wurare daban-daban a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta jihar Borno bisa bayanan sirri da bayanan da aka tattaro ta sama.

DA ƊUMI ƊUMI: INEC Ta Amince Da Takarar Pantami Da Abdulsalam Gwarzo A Zaɓen 2027

Goni ya ce bayanan da aka tattaro bayan hare-haren sun nuna cewa an kashe ‘yanta’adda 26 yayin da ‘yanta’adda shida suka jikkata sosai.

‘Yanayi mara kyau’ ne ya yi sanadin ɗaukewar numfashin masu hakar ma’adinai 37 a Nijeriya

‘Yanayi mara kyau’ ne ya yi sanadin ɗaukewar numfashin masu hakar ma’adinai 37 a Nijeriya

Advertisement

“A ƙarin samame na ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 2026, ɓangaren sojin ruwa na sansanin sojin ruwa da ke yankin Tafkin Chadi da aka tura Baga, ya kai samame kan ‘yanta’adda a yankin Tafkin Chadi,” in ji sanarwar.

“Bayanai na farko-farko sun nuna cewa an kashe ‘yanta’adda takwas, goma kuma sun ji rauni mataki daban daban,” a cewar Kyaftin Goni.

A wani ɓangaren kuma sanarwar ta ce wani samamen sama na sojin Nijeriya ya katse yunƙurin ɗana bam a kan hanya da wasu ‘yanta’adda suka yi, inda ya kashe ‘yanta’adda takwas tare da lalata motoci da baburansu da kayayyakin haɗa bama-bamai.

Sanarwar ta ce aikin ya hana ‘yanta’addan aikata aika-aikarsu, tana mai cewa waɗannan nasararorin sun nuna matsin da sojojin ke yi wa ‘yanta’addan ta hanyar hare-hare bisa bayanan sirri, lamarin da ke taƙaita aika-aikarsu kan al’ummomin arewa maso gabashin ƙasar.

 

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending