Connect with us

News

An Kwantar Da Dalibai 64 A Asibiti Bayan Shan Maganin Cutar Bilharzia A Katsina

Published

on

Majalisar dokokin Jihar Katsina ta amince da ƙirƙiro gundumomi guda shida a jihar
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Dalibai 64 na Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Batagarawa, a Jihar Katsina, sun kwanta asibiti bayan sun nuna alamun rashin lafiya jim kaɗan bayan shan magungunan cutar fitsarin jini, wato Bilharzia.

An garzaya da daliban zuwa Babban Asibitin Ahmadi Rimi da Asibitin Mata da Yara na Turai Yar’Adua, duk a cikin birnin Katsina, bayan sun fara amai, ciwon ciki da kuma jiri.

NCDC: Ebola Na Iya Tilasta Dage Zaben 2027 Idan Ta Yadu Sosai 

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin daliban sun suma kafin a kai su asibiti.

Daraktan Babban Asibitin Ahmadi Rimi, Dakta Auwal Sani, ya tabbatar da cewa an kawo wasu daga cikin daliban a sume, amma ya ce suna samun sauƙi sakamakon jinyar da ake yi musu.

NCDC: Ebola Na Iya Tilasta Dage Zaben 2027 Idan Ta Yadu Sosai 

Advertisement

Wasu daga cikin daliban da abin ya shafa, Abubakar Muhammad Khairi da Hassan Muhammad, sun shaida wa wakilin CHANNELSTV cewa an ba su magungunan ne bayan an auna tsayinsu.

Sun ce adadin ƙwayoyin maganin da aka ba daliban ya bambanta, inda aka ba wasu ƙwayoyi uku, wasu biyu, wasu kuma ƙwaya ɗaya.

Sai dai har yanzu ba a fayyace ƙa’idojin da aka bi wajen ƙayyade adadin maganin da aka bai wa kowane ɗalibi ba.

Wani mahaifi, Malam Ma’aruf Sani, wanda ya ziyarci ’ya’yansa a asibiti, ya ce sun samu sauƙi daga matsalolin lafiyar da suka fuskanta.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na Jihar Katsina, Yusuf Sulaiman Jibia, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce dukkan daliban da abin ya shafa sun warke, kuma ana shirin mayar da su makaranta.

“Daliban da abin ya shafa sun warke sarai, kuma muna shirye-shiryen mayar da su makaranta,” in ji shi.

Advertisement

Kwamishinan ya bayyana cewa jami’an kula da lafiya a matakin farko ne suka gudanar da shirin bayar da magungunan tare da haɗin gwiwar Karamar Hukumar Batagarawa.

Ya ce gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin, yana mai tabbatar wa iyaye da mazauna yankin cewa babu abin da zai sa su firgita.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending