Connect with us

News

NCDC: Ebola Na Iya Tilasta Dage Zaben 2027 Idan Ta Yadu Sosai 

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta ce za a iya dage babban zaɓen shekarar 2027 idan barkewar cutar Ebola ya yaɗu a Najeriya zuwa matakin da zai iya sanya gudanar da zaɓen cikin haɗari.

Darakta-Janar na hukumar, Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV inda aka tattauna kan barkewar cutar.

Dakarun Soji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sai dai Idris ya jaddada cewa a halin yanzu babu buƙatar dage zaɓen, yana mai fatan cewa lamarin ba zai taɓarɓare har ya kai ga hakan ba.

An tsara fara babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 a watan Janairu, yayin da jam’iyyun siyasa da masu neman takara suka fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen.

Shugaban NCDC yace sun daɗe suna sanya ido kan halin da barkewar cutar Ebola take ciki a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), kafin bullarta a Najeriya.

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumomin lafiya sun yi hasashen yiwuwar cutar ta shigo Najeriya saboda yawan zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashe.

Haka kuma, shugaban NCDC ya yi watsi da yiwuwar amfani da barkewar cutar a matsayin siyasa, yana mai cewa bai kamata a mayar da matsalolin lafiya wata hanya ta cimma muradun siyasa ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending