Connect with us

News

Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna

Published

on

IMG 20261020 125328 684
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wasu matasa daga Unguwar Gama, da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, sun yi kira ga Majalisar Dokokin jihar da ta binciki tare da ɗaukar matakin da ya dace kan ɗan majalisar mai wakiltar Nassarawa, Bello Ali Yusuf, bisa zargin nuna rashin girmamawa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Matasan, waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyar Concerned Gama Youth, sun yi kiran ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026.

Rushe Gidan Sha’aban: Lauya Ya Yi Zargin An Saɓa Wa Umarnin Kotu

Sun bayyana rashin jin daɗinsu kan wani faifan bidiyo da suka ce ya nuna ɗan majalisar yana riƙe da kunnen zomo mai rai a gaban magoya bayansa, abin da suka fassara a matsayin yunƙurin yi wa gwamnan ba’a.

A cewarsu, irin wannan hali bai dace da al’adun al’ummar Gama da ƙa’idojin dimokuraɗiyya ba, tare da bayyana damuwarsu kan yiwuwar lamarin ya haifar da rashin jituwa a tsakanin al’umma.

Ƙungiyar ta kuma jaddada goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana mai yaba wa gwamnatin jihar kan ayyukan raya ƙasa da ta gudanar a yankin.

Advertisement

Matasan sun ba da misali da hanyar da ta haɗa Gwagwarwa da Gama Hotel, wadda suka ce ta inganta zirga-zirga, ta bunƙasa kasuwanci tare da sauƙaƙa rayuwar mazauna yankin.

 

Sun kuma yi kira ga shugabannin al’umma da sauran mazauna Gama da su ba da muhimmanci ga zaman lafiya, haɗin kai da bin doka da oda.

A ƙarshe, Concerned Gama Youth ta buƙaci Majalisar Dokokin Jihar Kano da ta binciki zarge-zargen tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa dokokinta.

Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu martanin Bello Ali Yusuf kan zarge-zargen da aka yi masa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending