Connect with us

News

AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano 

Published

on

IMG 20261014 114319 230

Ƙungiyar Anniswan Women Health Initiative (AWOHI) ta raba kayan tallafi ga mazauna Gidan Kula da Tsofaffi da ke Shahuci, a Jihar Kano, a wani yunƙuri na inganta lafiyarsu, walwalarsu da yanayin rayuwarsu.

Kayayyakin tallafin sun haɗa da kayan abinci, man shafawa, sabulu, bututun alwala da sauran muhimman abubuwan buƙatun yau da kullum.

IMF Ya Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur

Daraktar Gudanarwa ta ƙungiyar, Maryam Rabiu Muhammad, ce ta bayyana hakan yayin ziyarar da ƙungiyar ta kai gidan, inda ta ce manufar ziyarar ita ce ƙarfafa alaƙa da cibiyar tare da gano hanyoyin da za a bi wajen inganta rayuwar tsofaffin.

Ta ce ƙungiyar ta ƙaddamar da shirin da ta kira “Our Elders, Our Heritage” (Tsofaffinmu, Gadonmu) domin tabbatar da cewa tsofaffi sun samu kulawa, girmamawa da damar rayuwa cikin walwala.

A cewarta, shirin zai mayar da hankali wajen samar da kayan masarufi, kayayyakin tsafta, tufafi da sauran muhimman abubuwan buƙata ga tsofaffi, musamman waɗanda ke zaune a gidajen kula da tsofaffi ko kuma ba sa samun isasshen tallafi daga iyalansu.

Advertisement

Maryam ta ƙara da cewa shirin zai kuma ƙunshi wayar da kan jama’a kan lafiyar tsofaffi, tare da shirya duba lafiyarsu ta hanyar haɗin gwiwa da ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

Ta ce za a kuma taimaka wajen tura tsofaffin da ke buƙatar ƙarin kulawar likitoci zuwa wuraren da suka dace, domin tabbatar da cewa sun samu kulawar da suke buƙata.

Baya ga batun lafiya, daraktar ta bayyana cewa shirin zai ba tsofaffin damar ba da labaran abubuwan da suka faru da su a rayuwa, tare da raba hikimominsu da al’adunsu ga matasa domin kiyaye tarihi da al’adun al’umma.

Da take tsokaci kan ziyarar, Maryam Musa, jami’a a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), ta yi maraba da shirin ƙungiyar, tana mai cewa gwamnati da hukumar suna maraba da shirye-shiryen da ke da manufar tallafa wa al’umma.

Ta ce irin waɗannan ayyuka na taimakawa wajen inganta walwalar mutanen da ke buƙatar kulawa ta musamman, musamman tsofaffi, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin sa-kai.

Taron ya kuma samu halartar wakilin Ma’aikatar Jin Ƙai da Rage Talauci ta Jihar Kano.

Advertisement

AWOHI ta bayyana aniyarta ta haɗa kai da hukumomin gwamnati, cibiyoyin lafiya, kamfanoni masu zaman kansu da masu hannu da shuni domin tabbatar da dorewar shirin da faɗaɗa ayyukansa.

Ƙungiyar ta jaddada cewa tsofaffi sun cancanci kulawa da girmamawa, tare da kira ga al’umma da su ba da gudummawa wajen inganta rayuwarsu da tabbatar da cewa ba a bar su a baya ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending