Connect with us

Ra'ayi

KANO PENSION APP: OGP Ta Kara Tabbata A Kano   —Yayin da OGP ke kara karfafa alaka da ‘yan jarida 

Published

on

Kano Governor Yusuf
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Abba Anwar

Shekaru da yawa, Open Government Partnership, wato OGP, a Kano kamar wani bakon abu ne kawai. Bayyana gaskiya. Rikon amana. Shigar da jama’a harkokin mulki a dama da su. Bayyana yadda ake kashe kudi. Samun bayanai.

Kalmomi masu kyau. A cikin tarurruka. A cikin sanarwa. A cikin tsarin aiki na jiha. Kalmomi da suke da kyau a kan takardu, amma watakila ba sa saka abinci a teburin tsohon mutum.

Ka tambayi tsohon mai ritaya a Fagge mene ne OGP, zai kalle ka, ya gyara hularsa, ya tambaye ka tambaya mai sauki, “Zai biya min kudin sallama ta a matsayin tsohon ma’aikaci, wato gratuity na?”

A ranar Litinin, 16 ga Nuwamba 2026, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amsa masa. Ba da taron karawa juna sani ba (workshop). Ba da wani kalar taron ba. Da wata App. App din da ta kawo karshen bin layi.

Kano State Pension Fund Trustees Pensioner Verification Application. A Google Play Store. Kyauta. Mai sauki.

Advertisement

Ka sauke ta. Ka tantance kanka. Daga gidanka. Kana Kano? Ka tantance. Kana Legas? Ka tantance. Kana London, Amurka, China, Saudi Arabiya? Ka tantance.

Babu sauran tafiya zuwa Kano. Babu sauran tsayawa a layi a karkashin rana kana da shekaru 70. Babu sauran kwana a tashar mota saboda ka zo tantancewa aka ce maka ka dawo gobe. Babu sauran biyan dillalai su taimaka maka ka karbi kudinka. Babu sauran “ka dawo gobe, ka dawo mako mai zuwa, ka dawo shekara mai zuwa.”

Wannan App guda daya ya yi abin da tarurrukan OGP da dama ke kokarin yi. Ya dauki iko daga ofis ya ba wa dan kasa. Wannan shi ne OGP. A zahiri. Ba a takarda ba.

To mene ne OGP din kuma a yadda ya zo kuma a yadda yake? An kirkiro shi a 2011 a matsayin hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci, kungiyoyin jama’a da ‘yan kasa. Najeriya ta shiga a 2016. Kano ta shiga a 2017, ta zama mamba a 2018.

Falsafarsa mai sauki ce, amma mai karfi a Najeriya:

1. Gwamnati kada ta boye.

Advertisement

2. Dan kasa kada ya roka.

3. A raba iko, kada a tara shi a wuri daya.

Tsarin Aiki na Jiha na OGP, wato Action Plan, na Kano na 2024-2026, wanda Gwamna Yusuf ya sanya hannu, ya lissafa alkawura bakwai don tabbatar da hakan, bayyana kashe kudi, samun bayanai, shigar da ‘yan kasa, samun adalci, yaki da cin hanci, inganta ayyuka, da sauyin yanayi.

Tsawon lokaci, wadannan alkawura ne a takarda. A karkashin Yusuf, suna zama abubuwa a wayoyin mutane.

Da farko aka zo da Ma’aikatar Saye da Sayarwa ta Jama’a, don bayyana yadda gwamnati ke kashe kudi. Domin kada a bayar da kwangiloli a duhu.

Sai aka zo da Kano State Integrated Projects Monitoring System (KSIPMS), inda kowane mazaunin Kano zai iya bibiyar aikin gwamnati a zahiri, kasafinsa, lokacinsa, ci gabansa. Ba sai ka zama kwamishina ba kafin ka san abin da ke faruwa a mazabarka.

Advertisement

Sai aka zo da Fix Kano App inda dan kasa zai iya kai rahoton hanya da ta lalace, famfo da ya bushe, asibitin da ya mutu, ya kuma bibiyi martanin gwamnati daga lokacin da ya aike zuwa lokacin da aka warware. Ka bayar da rahoto, ka biyo, ka gani.

Yanzu kuma, Pension Verification App. Apps hudu. Falsafa daya. Ba sai ka san wani a Gidan Gwamnati ba kafin Gidan Gwamnati ta yi maka hidima.

Ina ganin Hon. Musaddiq Kabir Adam, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan OGP, kuma a lokaci guda, Kodinetan OGP na Jiha, zai iya zama mutumin da ya fi kowa farin ciki a nan. SSA mai jajircewa, wanda ya yi imani da ingantaccen tsarin OGP. Haka nan a cikin kwamitin gudanarwa ma na Jiha an samu kwararru kuma jajirtattun gwaraza.

Hakan ne ya sa Sakatariyar OGP ta Kasa ta yabi Kano, kuma shi ya sa Kano ta tashi daga matsayi na 11 zuwa matsayi na 4 a matsayin OGP na kasa. Shi ya sa aka gayyaci Kano ta nuna gyare-gyarenta a Taron OGP na Duniya mai zuwa.

Amma matsayi ba shi ne labarin ba. Tsohon mutum shi ne labarin. Pension App ita ce labarin OGP mafi tsabta a Kano.

Idan kana son fahimtar OGP, a aikace, ba lallai sai ka je taron ba. Ka je ka zauna da mai ritaya wanda ya tantance kansa a wayarsa.

Advertisement

Duba wannan ci gaba ta idon OGP, daya bayan daya:

1. Bayyana Gaskiya – Yanzu zaka iya ganin abin da gwamnati ke yi.

A da, mai ritaya bai san ko sunansa yana cikin jerin wadanda za a biya ba. Bai san ko fayil dinsa ya bata a wani sako ba. Bai san ko wani ya karbi kudinsa ya sanya hannu a madadinsa ba. Yana rayuwa cikin duhu, kuma duhu ne inda cin hanci ke girma.

Yanzu, tantancewa ta zama ta dijital. Biyan albashi ya zama na’ura mai kwakwalwa gaba daya. Daukar hoton yatsa ya kammala. Kowane suna an dauka. Kowane yatsa an dauka. Kowane biya ana iya bibiyarsa. Kowane sako yana shiga bankin mai ritaya kai tsaye, ba hannun dillali ba.

Gwamnan da kansa ya ce an gina tsarin ne don “kawar da cikas na ofis da kuma tabbatar da inganci.”

A bayyane, babu sauran ‘yan sojan gona masu cin abincin ainihin ‘yan ritaya. Babu sauran fayiloli da ke bacewa. Babu sauran “sunanka ba ya nan, ka dawo wata mai zuwa.”

Advertisement

2. Rikon Amana: Yanzu za a iya rike gwamnati da alkawarunta.

A ranar 16 ga Nuwamba, Gwamna fitar da Naira biliyan 5 na yan fansho, wato kashi na 7. Ya kuma bayar da kwanan wata. Afrilu 2027. Ya ce, “A watan Afrilu 2027, Gwamnatin Jihar Kano za ta iya biyan kowane kobo.”

Da Naira biliyan 37 da aka riga aka biya daga cikin Naira biliyan 48 na bashin da aka gada, wato kashi 77.1% an gama. Ragowar Naira biliyan 11 yanzu alkawari ne na jama’a, da wa’adin jama’a, a kan App na jama’a.

Wannan shi ne kyawunsa. A da, gwamnati za ta iya yin alkawari ta manta. Yanzu, kungiyoyin jama’a, ‘yan jarida, da ‘yan ritaya da kansu za su iya kirgawa. Za su iya bude App. Za su iya duba kashin biya. Za su iya tambaya: Ka ce Afrilu 2027, ina muke yanzu?

App din ta sanya Gwamna ya zama mai amsa tambaya ba ga Abuja kawai ba, ba ga Sakatariyar OGP kawai ba, amma ga tsohon mutum a Dala wanda ke jiran sakon bankinsa. Wannan rikon amana ne daga kasa, ba daga sama ba.

3. Shigar da Jama’a – Tsohon mutum yanzu mai mutunci ne, ba maroki ba. OGP ta ce ‘yan kasa kada su zama masu kallo kawai. Dole su zama masu shiga al’amura. Dole su hada kai su gina gwamnati. Ikon hada kai.

Advertisement

Me ya fi dadi fiye da tsoho dan shekara 80 da ya tantance kansa daga dakinsa a Rano, ba tare da ya roki ma’aikaci ba? Me ya fi dadi fiye da wacce mijin ta ya rasu a Gaya, wacce ba ta iya biyan kudin mota zuwa Kano, ta tantance kanta daga wayar danta ta karbi kudin mutuwar mijinta?

Me ya fi dadi fiye da Kungiyar ‘Yan Ritaya ta Najeriya, karkashin jagorancin Kwamared Godwin Ikechukwu-Abumisi, tana zaune a tebur da gwamnati, ba a wajen kofa tana ihu ba?

Me ya fi dadi fiye da Kano ta zabi wakilan kungiyoyin jama’a zuwa Kwamitin Gudanarwa na OGP ta hanyar zabe na gaskiya, wanda Sakatariyar OGP ta Kasa ta sa ido, da daidaito – gwamnati da kungiyoyin jama’a, gefe da gefe?

Yanzu tunanin ya canza. Mai ritaya ba ya jin kamar maroki. Yana jin kamar mai mallaka. Domin shi mai mallaka ne. Kudinsa ne. Hakkinsa ne.

4. Hada Kowa – Ba a bar kowa a baya saboda ya tsufa, ya talauce, ko yana nesa ba. OGP ba don masu ilimi, matasa, ko masu waya kawai ba ce. Ta kowa ce. Musamman masu rauni.

Ka yi tunani. Wa ya fi shan wahala daga tantancewa ta jiki? Tsofaffi. Marasa lafiya. Talakawa. Gwauraye. Mutumin da ya yi ritaya a 2012 yanzu yana zaune a kauye babu hanya.

Advertisement

Pension App ta ce musu, ku na da muhimmanci. Ba sai kun yi tafiya ba. Ba sai kun kashe Naira 20,000 na mota don karbar Naira 50,000 na gratuity ba. Ba sai kun zama masu karfi ba kafin a yi muku hidima.

5. Yaki da Cin Hanci – Fasaha ta yi waje da dillali. Kowane dan Najeriya ya san dillali. Mutumin da ke bakin kofa yana cewa “ka kawo wani abu, zan taimaka maka ka ga oga.” Mutumin da ke cewa “fayil dinka ya bata, amma zan iya samowa.”

Pension App ba ta da kofa. Ba ta da oga da za a gani. Ba ta da fayil da zai bata. Idan tantancewa ta yatsa ce, ba za a iya karya ta ba. Idan biya kai tsaye ne zuwa banki, ba za a iya karkatar da shi ba. Idan biyan albashi na’ura ce, ba za a iya saka sunan fatalwa ba.

A watan Afrilun 2025, Shugaban Zartarwa na Pension Fund Trustees, Alhaji Habu Muhammad Fagge, ya ce Asusun ya gaji wani yanayi mai matukar damuwa, inda ‘yan ritaya ke fuskantar raguwar kudi ba bisa ka’ida ba, wani lokaci suna rasa rabin hakkinsu, kuma gwamnatocin baya sun yi rance sosai daga asusun fansho.

App din ita ce amsar wannan tarihi. Kulle ce a kofa. Tana cewa, ba za a sake barin kudin mai ritaya ya bace a ofis ba. Wannan yaki da cin hanci ne, ba ta hanyar kama ba, amma ta hanyar tsari.

6. Samun Bayanai – Hakkinka na sani, a hannunka. OGP ta ce ‘yan kasa suna da hakkin sanin abin da gwamnati ke yi da kudinsu.

Advertisement

A da, mai ritaya sai ya rubuta wasika kafin ya san halinsa. Yanzu, ya bude wayarsa.

A da, dan jarida sai ya roka kafin ya samu bayanai. Yanzu, Gwamna yana sanar da kowane kashin biyan yan fansho a fili: Kashi na 1 Naira biliyan 6, na 2 Naira biliyan 5, na 3 Naira biliyan 5, jimilla Naira biliyan 16 ga ‘yan ritaya 6,886, sai Naira biliyan 32, sai Naira biliyan 37. A bayyane. Ana iya kirgawa. Ana iya tabbatarwa.

Samun bayanai ba abu ne na neman Freedom of Information ba. Sako ne a wayarka.

7. Fasaha da Kirkire-kirkire Don Hidima – Sabon fagen OGP.

A watan Nuwamba 2026, Kodinetan OGP na Kano, Musaddiq Kabir Adam, ya gaya wa ‘yan jarida a Dutse cewa Kano tana ba da fifiko ga AI don Gudanarwa, kasafin kudi na bayyane, hada matasa da shigar da ‘yan kasa.

Pension App ita ce wannan fifiko a aikace. Tana amfani da fasaha don warware matsalar dan Adam, nesa, tsufa, talauci, da cin hanci.

Advertisement

Mai ritaya wanda ba zai iya tafiya ba yanzu za a iya tantance shi. Mace wacce ba za ta iya biyan mota daga Gaya zuwa Kano ba yanzu za a iya tantance ta. Malamin da ya yi ritaya yana zaune da dansa a can wata kasa yanzu za a iya tantance shi. Fasaha ba ta maye gurbin tausayi ba. Fasaha ta isar da tausayi.

OGP a jihohi da dama a Najeriya ta zama biki. An kaddamar da Kwamitin Gudanarwa. An dauki hoto. An fitar da sanarwa. Babu abin da ya canza a kauye. Kano tana kokarin karya wannan al’ada.

Idan mai ritaya ya bude wayarsa ya ga sakon gratuity dinsa, ba sai ya san mene ne OGP ba. Yana jin mene ne OGP.

Idan matashi ya bude Fix Kano App ya kai rahoton rijiyar da ta lalace ya ga gwamnati ta amsa, ba sai ya haddace Tsarin Aiki na 2024-2026 ba. Yana rayuwa da shi.

Idan dan jarida ya bude KSIPMS ya duba kasafin aiki, ba sai an yi masa lacca kan bayyana kashe kudi ba. Yana aikata shi.

Wannan shi ne fa’idar Pension App ga OGP a Kano. Ta mayar da OGP daga takarda zuwa zahiri. Ta tabbatar da cewa OGP ba game da bude fayiloli ba ne. Game da bude kofofi ne. Ba game da gwamnati tana magana da ‘yan kasa ba ne. Game da gwamnati tana sauraron ‘yan kasa ne, kuma ‘yan kasa suna rike gwamnati da kalmarta, da shaida a hannunsu.

Advertisement

OGP ta Kano tana daga cikin mafi kyau, ba a Najeriya kawai ba, har ma a fadin Afirka kudu da Sahara. Yayin da Gwamnan ke da himma kuma da zuciyar aikin, Kodinetan Jiha ba wai yana daidaitawa da kyau ba kawai, har ma ya san da wane da wane zai daidaita tare da kuma tsara dabarun samun nasara. Tare da dukkan ragowar yan kwamitin gudanarwa na OGP din. Mutane kwararru da kishin kasa.

Taron da aka yi kwanan nan a Dutse, Jihar Jigawa, a ranar 14 ga Nuwamba, 2026, wanda Kano OGP ta shirya, a matsayin Taron Wayar da Kai na Rana Daya ga Manema Labarai na Kano, ya bayar da haske game da sahihin himmar Mai Girma Gwamna da dukkan Kwamitin Gudanarwa na OGP, wajen tura falsafar OGP zuwa matsayi mafi girma.

 

Anwar ya rubuto daga Kano

Juma’at, 20 ga Nuwamba, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending