Connect with us

News

IMF Ya Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur

Published

on

Tinubu 1000x600

IMF Ya Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur

 

 

 

 

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya gargaɗi Najeriya kan maido da cikakken tallafin man fetur, yana mai cewa hakan zai ƙara yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.

Advertisement

Jaridar TheCable ta rawaito cewa daraktan sashen harkokin kuɗaɗen gwamnati na IMF, Rodrigo Valdés, ya ce tallafin man fetur na bai ɗaya yana da tsada, kuma galibi masu kuɗi ne suka fi amfana da shi.

Jami’an  Civil Defence Sun Kama Likitan Bogi Bisa Zargin Zubar Wa Da Mata Ciki A Kwara

Valdés ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na IMF da Bankin Duniya a Bangkok, Thailand, ranar Laraba.

Ya ce tallafin makamashi ya jawo wa ƙasashe kashe kuɗaɗen da suka kai tsakanin kashi 1 zuwa 1.5 na GDP a shekarar 2026.

Ya shawarci gwamnatoci su mayar da hankali kan tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar rage kuɗin sufuri, samar da abinci ga ɗalibai a makarantu da taimaka wa manoma.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta sanar da rangwamen farashin man fetur na kwanaki 30 a gidajen mai na NNPC domin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar mai.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending