Labarai
An Sake Tsintar Wani Jariri Sabuwar Haihuwa A Ƙofar Na’isa Da Ke Kano

Rahotanni sun bayyana cewa an sake samun wani jariri a unguwar Kofar Na’isa da ke cikin birnin Kano, ƙasa da kwanaki biyu bayan samun rahoton tsintar wasu jarirai ƴan tagwaye biyu a unguwar Dorayi Unguwar Bello, da ke Ƙaramar hukumar Gwale.
Ɗan gwagwarmayar nan Comrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samu jaririn ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau.
KANO: An tsinci ‘Yan Tagwayen Jarirai Sabuwar Haihuwa A Yankin Dorayi Unguwar Bello
A cewarsa, wani yaro ne ya buɗe wata leda da aka ajiye a wurin, inda ya tarar da jaririn sai dai ana kyautata zaton cewar jaririn ya rasu.
Ƴan tagwayen jariran da aka tsinta a yankin Ɗorayi, yanzu haka an tabbatar da rasuwa ɗaya daga cikin su.
Lamarin dai ya ƙara tayar da hankalin al’umma kan yadda ake samun rahotannin ajiye jarirai a wasu sassan birnin Kano.
