Labarai
Kwankwaso Ne Ya Sa Na Rantse Da Alƙur’ani Za Mu Koma Jam’iyyar APC —Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya tura shi wajen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin yin alƙawarin komawa jam’iyyar APC idan aka samu nasara a shari’ar zaɓen gwamnan Kano ta 2023.
Abba Kabir ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da BBC HAUSA, inda ya ce Kwankwaso ya buƙaci ya je wajen Tinubu, har ma ya yi rantsuwa da Alƙur’ani kan alƙawarin komawarsu APC.
An Kama Ɗan Wasan Golf Ɗan Afirka Ta Kudu Da Mai Girki ’Yar Kenya Da Tabar Wiwi Kilo 50 A Legas
Gwamnan ya ce bayan zaɓen 2023, sun tattauna da Tinubu tare da cimma yarjejeniya cewa idan shugaban ƙasar bai tsoma baki a shari’ar zaɓen Kano ba, za su koma APC bayan samun nasara.
Ya ce Kwankwaso ne ya tura shi wajen Tinubu domin tabbatar da wannan alƙawari, inda ya ce idan ya zama dole, ya ɗauki Alƙur’ani ya rantse cewa za su koma jam’iyyar APC idan Allah ya ba su nasara.
Abba Kabir ya ƙara da cewa daga baya Kwankwaso ya yi watsi da yarjejeniyar da suka cimma, duk da cewa shi ya jagoranci shirin da kuma alƙawarin.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa sau da dama Kwankwaso ya gana da Tinubu, sannan ya tura tawaga domin tattauna batun komawarsu APC.
Ya ce ba ya ganin komawarsa APC a matsayin butulci ga Kwankwaso, domin a ganinsa, shi ne ya cika alƙawarin da aka ɗauka, yayin da tsohon jagoransa ya kasa yin hakan.
Abba Kabir ya koma APC a hukumance a ranar 26 ga Janairun 2026, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar 23 ga Janairu, matakin da ya haifar da babban sauyi a siyasar Kano tare da raba gari tsakaninsa da Kwankwaso.
Gwamnan ya kuma yi ƙarin bayani a tattaunawar kan saɓanin da ya shiga tsakaninsa da matarsa, Zainab Musa Kwankwaso, da kuma ƙalubalen tsaro da jihar Kano ke fuskanta.
