News
Messi Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Argentina Ƙwallo
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Lionel Messi, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Argentina ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa, bayan shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar ƙasar.
Messi, mai shekara 39, ya sanar da matakin ne a ranar Litinin ta hannun wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya ce matakin ya kasance mai raɗaɗi, amma ya fahimci cewa lokaci ya yi da zai ajiye wa matasa gurbi a tawagar ƙasar.
An Cafke Wata Mahaifiya Bisa Zargin Kai Wa Ɗanta Miyagun Ƙwayoyi A Gidan Yari
Ya fara buga wa babbar tawagar Argentina wasa a shekarar 2005, kuma ya zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan buga wa ƙasar wasa, bayan da ya kai wasanni 207, inda ya zura ƙwallaye 125 tare da taimakawa wajen cin wasu 65.
A tsawon lokacin da ya yi yana wakiltar Argentina, Messi ya taimaka wa ƙasar ta lashe manyan kofuna, ciki har da Copa América ta 2021 da 2024, da kuma Kofin Duniya na 2022 da aka gudanar a Qatar. Haka kuma, ya lashe lambar zinare a gasar Olympics ta 2008 da kuma kofin Finalissima na 2022.
Messi ya kuma jagoranci Argentina zuwa wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2026, inda Spain ta doke ta da ci 1-0 a wasan ƙarshe da aka buga a Amurka a watan Yuli. Wannan ne ya zama wasan ƙarshe da ya bugawa Argentina.
A cikin saƙonsa, Messi ya ce ya kasance yana ba da dukkan ƙarfinsa ga tawagar Argentina, yana fafutukar ganin ƙasar ta samu nasara tare da faranta ran magoya bayanta.
Ya ce shawarar yin ritaya ta kasance mai wahala a gare shi, amma ya yi imanin cewa yanzu ne lokacin da ya kamata ya bar matasa su samu damar nuna ƙwarewarsu a tawagar ƙasar.
Da wannan ritaya, Messi ya bar tarihi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ’yan wasan da suka taɓa wakiltar Argentina, tare da lashe manyan kofuna da dama da kuma kafa tarihi a fagen ƙwallon ƙafa na duniya.
