Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha

Published

on

Kano Governor Yusuf

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Talata, 1 ga Satumba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bai wa mazauna jihar damar gudanar da bikin Takutaha, wata muhimmiyar al’ada ta addini da ake gudanarwa duk shekara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Kafa Dokoki da Ayyukan Gwamnati, Abba A. Danguguwa, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Jihar.

“Ba Za Mu Bayar Da Ko Taku Daya Na Kasa Ba  Don Yin Burtali Ga Fulani Makiyaya” —Gwamnan Jihar Benue

Sanarwar ta ce ranar hutun ta yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1448 bayan hijira, inda ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da ayyana ranar a matsayin hutu.

Gwamnatin ta bayyana Takutaha a matsayin muhimmiyar al’ada mai alaka da addini da tarihi, wadda ke da matukar muhimmanci ga al’ummar Kano tare da kasancewa wani bangare na tarihin Musulunci na jihar.

Ta bukaci ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da ranar wajen addu’o’i da neman gafara, tare da rokon Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, kwanciyar hankali da ci gaba a Kano da Najeriya baki daya.

Advertisement

Sanarwar ta umurci shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su tabbatar da bin umarnin, sai dai ta ce ma’aikatan da ke kula da muhimman ayyuka za su ci gaba da aiki kamar yadda tsarin hukumominsu ya tanada.

 

STALLION TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending