News
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci masu talla da masu sana’ar jari bola da suka mamaye karkashin gadar Tal’udu da su gaggauta barin wurin, tare da gargadin cewa duk wanda ya ƙi bin umarnin zai fuskanci hukunci a gaban doka.
Shugaban Kwamitin Musamman na Yaki da Gina Haramtattun Abubuwa a Jihar Kano, Dr. Dalhatu Aliyu Sani, ne ya bayyana hakan yayin da yake duba aikin kwamitin a karkashin gadar Tal’udu a ranar Litinin.
Yan Bindiga Sun Hallaka Kanal Din Soja A Gidansa Da Ke Abuja
Ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kashe biliyoyin naira wajen gina gadoji na zamani domin kyautata fasalin birnin Kano, rage cunkoson ababen hawa, inganta muhalli da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda wasu ke amfani da karkashin gadojin wajen yin talla, sana’ar jari bola da sauran ayyukan da suka saba wa manufar gina wuraren.
Dr. Dalhatu ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar irin wadannan ayyuka ba.
> “Ba a ware wannan wuri domin yin talla ko sana’ar jari bola ba, haka kuma ba filin wasan kwallo ba ne. Duk wanda aka kama yana karya wannan doka za a gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada,” in ji shi.
Ya kuma bukaci al’ummar Kano su rungumi tsafta da kiyaye kadarorin gwamnati domin gina birni mai tsari da ingantaccen muhalli.
A yayin aikin kwamitin a yankin masana’antu na Chalawa, an kuma rufe wata karamar masana’anta bisa zargin mamaye filin wani ba bisa ka’ida ba. An umurci mai masana’antar da ya gabatar da takardun mallakar filin domin ci gaba da bincike.
