Connect with us

News

Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300

Published

on

Troops 1000x600

Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa shugaban ’yan ta’adda, tare da wasu mutum biyu da ake zargin mambobin ƙungiyarsa ne a Jihar Kaduna.

Dakarun sun kuma cafke wata mata mai shekaru 50 da ake zargi da safarar harsasai, da wani mutum da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayan tallafi da na’urorin sadarwa a wasu samame daban-daban.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Satar Wayar Hannu Guda 41 A Maiduguri

A ranar Laraba, 9 ga Satumba 2026, dakarun Sector 1 sun gudanar da samame a Dabar Dabo, wata maboyar da ake zargin ’yan ta’adda na amfani da ita a ƙaramar hukumar Kubau.

A yayin samamen, sojojin sun cafke wanda ake zargin shugaban ƙungiyar ’yan ta’addan ne tare da wasu mutum biyu. Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda aka kama.

A wani samame da aka gudanar a ƙaramar hukumar Igabi, sojojin sun cafke wata mata mai shekaru 50 bisa zargin safarar harsasai, bayan samun bayanan sirri kan motsin alburusai.

Advertisement

Rundunar ta ce an gano harsasai 300 a cikin jakar matar. Binciken farko ya nuna cewa ta yi tafiya daga Jihar Zamfara zuwa Lafiya, inda ake zargin ta karɓi harsasan domin kai su ga ’yan ta’adda a Birnin Gwari.

Haka kuma, a Birnin Gwari, dakarun Sector 1 tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na al’umma sun cafke wani mutum da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayan tallafi.

Sojojin sun ce an gano na’urorin sadarwa guda huɗu da ake zargin ’yan ta’adda na amfani da su daga hannun wanda ake zargin.

A cikin wata sanarwa, Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwar Sojoji ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce samamen na daga cikin ƙoƙarin rundunar na tarwatsa hanyoyin sadarwa da samar da makamai da kayan aiki ga ’yan ta’adda.

Ya ce dukkan waɗanda aka kama da kayayyakin da aka kwato suna hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.

Rundunar ta yaba wa jama’a bisa haɗin kan da suke bai wa jami’an tsaro, tare da kira gare su da su ci gaba da taka-tsantsan da kuma kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi ga hukumomin tsaro.

Advertisement

 

 

PRNIGERIA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending