Sports
Manchester United Ta Mallaki Filin Gina Sabon Filin Wasa Mai Daukar Mutane Dubu Dari
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ɗauki wani gagarumin mataki wajen cika burinta na gina sabon katafaren filin wasa na zamani, bayan da ta mallaki filin da ake buƙata domin gudanar da aikin.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na intanet, ta bayyana cewa ta sayi fili mai faɗin kadada 25, wanda ke da tazarar kusan mita 350 a arewa maso yammacin filin wasan Old Trafford na yanzu.
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Dukkan Kamfanonin Siminti Da Su Rage Farashi
Rahotanni sun nuna cewa sabon filin wasan da ake shirin ginawa zai iya ɗaukar mutane 100,000, lamarin da zai sa ya zama mafi girman filin wasa a faɗin Birtaniya idan aka kammala aikin.
Shirin gina sabon filin wasan na daga cikin ƙoƙarin da Manchester United ke yi na inganta kayayyakin more rayuwa da samar wa magoya bayanta ingantaccen yanayi na kallon wasanni.
Ana sa ran sabon filin wasan zai zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin wasanni a duniya, tare da ƙara wa yankin Manchester bunƙasar tattalin arziki da jawo baƙi daga sassa daban-daban na duniya.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
