Connect with us

Wassanni

Najeriya Ba Ta Kai Matsayin Da Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kofin Duniya Ba —Shugaban FIFA 

Published

on

B6NG73L Preview W 1 2026 11 23 483 768x512
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai matsayin da za ta iya karɓar bakuncin gasar cin kofin duniya a halin yanzu ba, saboda ƙarancin kayayyakin more rayuwa da ake buƙata domin gudanar da gasa mai girman haka.

Infantino ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na ARISE a Abuja ranar Litinin, inda aka tambaye shi ko Najeriya za ta iya karɓar bakuncin gasar cin kofin duniya.

An Sake Tsintar Wani Jariri Sabuwar Haihuwa A Ƙofar Na’isa Da Ke Kano

Ya ce ƙasar na buƙatar inganta muhimman kayayyakin more rayuwa, musamman filayen wasa, filayen jiragen sama da hanyoyin sufuri, domin ta cika ƙa’idojin da FIFA ke buƙata.

Sai dai shugaban FIFA ya nuna kyakkyawan fata cewa Najeriya za ta iya cimma wannan buri a nan gaba, yana mai cewa ƙasar na da albarkatu, ƙwazo da azamar da za su taimaka mata wajen cika waɗannan ƙa’idoji.

Infantino ya jaddada cewa duk da cewa Najeriya ba ta shirya karɓar bakuncin gasar a yanzu ba, akwai damar da za ta iya yin hakan a nan gaba idan ta inganta kayayyakin more rayuwarta.

Advertisement

 

 

THE CABLE 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending