Labarai
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Sama Tiriliyan 3 A Biyan Bashin Da Kanfanonin Samar Da Wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin kashe naira tiriliyan 3 da biliyan 3 wajen biyan basussukan da ke kan kamfanonin samar da wutar lantarki, domin magance wasu daga cikin matsalolin da suka addabi ɓangaren lantarki a Najeriya.
Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan yayin wata hira ta musamman da gidan talabijin na ARISE a ranar Litinin.
Najeriya Ba Ta Kai Matsayin Da Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Kofin Duniya Ba —Shugaban FIFA
Ministan ya ce shirin na daga cikin matakan da gwamnatin ke ɗauka domin magance ƙarancin kayayyakin more rayuwa, basussukan da suka taru a ɓangaren wutar lantarki da sauran ƙalubalen da ke hana inganta samar da lantarki a ƙasar.
Ya bayyana cewa gwamnatin na ƙoƙarin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da suka daɗe suna addabar ɓangaren, domin inganta samar da wutar lantarki da tabbatar da ingantaccen aiki a masana’antar.
