Connect with us

Labarai

INEC Za Ta Gwada Na’urar BVAS A Rumfunan Zabe 17,656 Ranar 28 Ga Nuwamba

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta zaɓi rumfunan zaɓe 17,656 a faɗin Najeriya domin gwada na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS gabanin babban zaɓen 2027.

Hukumar ta ce za ta gudanar da gwajin ne ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Sama Tiriliyan 3 A Biyan Bashin Da Kanfanonin Samar Da Wutar lantarki

Gwajin na da nufin tabbatar da ingancin na’urar BVAS wajen tantance masu zaɓe, da kuma gwada yadda ake aika sakamakon zaɓe ta intanet.

INEC ta bayyana cewa za a gudanar da gwajin ne a rumfunan zaɓe biyu daga kowace gundumar rajistar masu zaɓe guda 8,838 a faɗin ƙasar.

Sai dai binciken jerin sunayen rumfunan ya nuna cewa an samu 17,656, maimakon 17,676 da ya kamata a samu, wanda ke nuna ƙarancin rumfunan zaɓe 20.

Advertisement

Bayanan sun nuna cewa Kano ce kan gaba da rumfunan zaɓe 968, sai Katsina mai 718 da Oyo mai 702.

A gefe guda, Abuja ce ke da mafi ƙarancin rumfunan zaɓen da aka zaɓa, guda 124, sai Bayelsa mai 210 da Gombe mai 228.

Dangane da yankunan ƙasar kuwa, Arewa maso Yamma ce ke kan gaba da rumfunan zaɓe 4,002, kwatankwacin kashi 22.7 cikin 100 na jimillar rumfunan da aka zaɓa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending