Connect with us

Sports

Da Dumi-Dumi: Manchester United Ta Kori Mason Greenwood

Published

on

Mason Greenwood

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

 

Advertisement

Kungiyar Manchester United ta kori dan wasa Mason Greenwood daga kungiyar bayan ta kammala bincike akan dan wasan.

An yi watsi da tuhumar da ake yi wa dan wasan mai shekaru 21, gami da yunƙurin fyade da kai hari a ranar 2 ga Fabrairu.

Advertisement

Nyesom Wike ya yi barazanar rusa gidaje a ranarsa ta farko a ofishi

An sa ran cewa sanarwa za ta fito kafin fara gasar Premier da za su kara da Wolves a ranar Litinin amma aka jinkirta.

Yanzu dai dan wasan ba zai sake buga wa kungiyar wasa ba kuma lauyoyin kungiyar da na dan wasan zasu zauna domin soke kwangilar dan wasan.

Advertisement

Daman dai shawara game da makomar Greenwood a yanzu, ya rataya ne a wuyan babban jami’in zartarwar ƙungiyar Richard Arnold – kuma a halin yanzu ana kan matakin ƙarshe.

Greenwood bai buga wasa a United ba tun lokacin da aka tuhume shi kuma bai shiga filin atisayen kungiyar na Carrington ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending