News
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
Wani matashi mai suna Abdullahi Aminu, mai kimanin shekaru 18, ya rasa ransa bayan da ya fada cikin wani Ruwa a yankin Kofar Gabas, da ke Karamar Hukumar Danbatta a Jihar Kano.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar ranar Laraba, 12 ga Agusta, 2026.
Auren Zawarawa Da Gwamnatin Kano Ta Yi Haramun Ne — Sheik Hadi MaiHula
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga Agusta, da misalin karfe 3:28 na rana, bayan da Hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Aminu Lawan, wanda ya sanar da ofishin kashe gobara da ke Danbatta cewa dansa ya fada cikin wani ruwa.
Sanarwar ta ce jami’an sun samu nasarar gano matashin tare da fitar da shi daga cikin ruwan, amma yana cikin halin sume.
Sai dai, daga bisani aka tabbatar da cewa matashin ya mutu.
Hukumar ta ce daga nan aka mika gawar marigayin ga Sakataren Hakimin Danbatta, Alhaji Baba Ado Sarkin Bai, domin daukar matakan dasuka dace.
-
News19 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
