News
Jami’an Tsaro Sun Hallaka Ƴan Bindiga Sama Da 40 Tare Da Daƙile Wani Hari
Jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga bayan da suka hallaka wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da aka fi sani da Iliya Mai Rasha, tare da wasu ’yan bindiga sama da 40 a wani artabu da ya auku a ƙauyen Guga da ke Ƙaramar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa Iliya Mai Rasha, wanda ake zargi da jagorantar hare-hare, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da wasu yankunan da ke maƙwabtaka, na daga cikin manyan kwamandojin da suka jagoranci harin da aka kai ƙauyen Guga a ranar Lahadi.
Mutum 14 Sun Mutu Yayin Da Ake Zargin Mutum 441 Sun Kamu Da Cutar Kwalara A Filato
Rahotanni sun ce da misalin ƙarfe 5:40 na yammacin ranar 26 ga Yuli ne sama da ’yan bindiga 200 ɗauke da manyan makamai suka mamaye ƙauyen. An ce sun fito ne daga sansanoninsu da ke jihohin Katsina da Zamfara bisa umarnin wani shugaban ’yan bindiga mai suna Idi Abasu Aiki.
Sai dai da isarsu ƙauyen, sun gamu da ƙwaƙƙwaran martani daga haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro da ta haɗa da dakarun Brigade ta 17 ta Rundunar Sojin Najeriya, jami’an Katsina State Community Watch Corps (KSCWC) da kuma mafarauta, lamarin da ya haifar da mummunar musayar wuta.
Bayan doguwar fafatawa, ’yan bindigar sun fara ja da baya sakamakon asarar rayuka da suka yi. Majiyoyin tsaro sun ce sama da ’yan bindiga 40 ne aka kashe, ciki har da akalla manyan kwamandoji takwas.
Haka kuma, majiyoyin sun ce shugaban ’yan bindigar, Idi Abasu Aiki, ya samu munanan raunukan harbin bindiga, kuma ana kyautata zaton yana cikin mawuyacin hali.
Kashe Iliya Mai Rasha na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da jami’an tsaro suka samu a yaƙin da suke yi da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, inda aka daɗe ana neman sa bisa zargin jagorantar hare-hare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Majiyoyin soji sun ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da samame domin cafke ’yan bindigar da suka tsere, kwato makaman da suka bari da kuma rushe sansanoninsu domin hana su sake farfaɗowa.
Sai dai duk da wannan nasara, mafarauta biyar sun rasa rayukansu yayin arangamar, abin da ke nuna irin sadaukarwar da suke yi wajen taimaka wa jami’an tsaro wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Hukumomin tsaro da Gwamnatin Jihar Katsina sun yabawa dakarun soji, jami’an KSCWC da mafarauta bisa jarumtaka da haɗin kan da suka nuna wajen daƙile harin, tare da jaddada aniyarsu ta ci gaba da fatattakar ’yan bindiga da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
