Connect with us

News

Mutum 14 Sun Mutu Yayin Da Ake Zargin Mutum 441 Sun Kamu Da Cutar Kwalara A Filato

Published

on

Cholera outbreak 661x370

Gwamnatin Jihar Filato ta ce mutum 14 sun rasu, yayin da ake zargin mutum 441 sun kamu da cutar kwalara tun bayan ɓarkewar cutar a watan Yunin 2026.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Nicholas Ba’amlong, ya bayyana hakan a Jos ranar Litinin. Ya ce an tabbatar da mutum 20 sun kamu da cutar ta hanyar gwajin farko (RDT), yayin da gwajin dakin gwaje-gwaje ya tabbatar da mutum shida.

‘Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 200 Kuɗin Fansa Domin Sakin Alƙalin Babbar Kotun Kebbi

A cewarsa, cutar ta shafi ƙananan hukumomi huɗu, unguwanni 25 da kuma ƙauyuka 107.

Ya ce mutum uku ne kawai ke ci gaba da karɓar magani a asibiti, dukkansu daga Ƙaramar Hukumar Jos North, lamarin da ya nuna cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na fara yin tasiri.

Ba’amlong ya ce an fara gano cutar ne a Ƙaramar Hukumar Mangu a farkon watan Yuni, wanda ya sa gwamnatin jihar ta ƙaddamar da matakan gaggawa tare da haɗin gwiwar Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), ƙananan hukumomi da sauran abokan hulɗa.

Advertisement

Ya bayyana cewa Mangu, wadda ita ce cibiyar farko ta ɓarkewar cutar, ta samu mutum 53 da ake zargin sun kamu da kwalara. Daga cikinsu, gwajin RDT ya tabbatar da mutum 10, yayin da gwajin dakin gwaje-gwaje ya tabbatar da mutum huɗu. Haka kuma mutum 10 sun rasu.

Sai dai ya ce tun daga ranar 22 ga Yulin 2026 ba a sake samun sabon mai ɗauke da cutar a Mangu ba.

A Jos North kuwa, an samu mutum 277 da ake zargi sun kamu da cutar, mutum bakwai sun tabbatar ta gwajin RDT, mutum ɗaya ta gwajin dakin gwaje-gwaje, yayin da mutum huɗu suka mutu.

A Ƙaramar Hukumar Jos South kuma, an tabbatar da mutum ɗaya ya kamu da cutar, an yi masa magani kuma an sallame shi ba tare da an samu mace-mace ba.

Shi ma Barkin Ladi ya samu bullar cutar a ranar 16 ga Yuli, inda aka samu mutum 23 da ake zargi sun kamu da ita, mutum biyu suka tabbatar ta gwajin RDT, ba tare da an samu mace-mace ba.

Kwamishinan ya ce duk da cewa an dakile yaɗuwar cutar a Mangu, har yanzu ana samun sababbin masu kamuwa da ita a Jos North, Jos South da Barkin Ladi.

Advertisement

Ya danganta yawan mace-macen da aka samu da jinkirin zuwa asibiti domin neman magani, inda ya buƙaci jama’a su garzaya cibiyar lafiya da zarar sun fara ganin alamomin cutar.

Ba’amlong ya ce gwamnatin jihar ta ƙara ƙaimi wajen gano sabbin masu cutar, sa ido kan yaɗuwarta da kuma samar da magunguna da kayan jinya. Haka kuma ana wayar da kan jama’a ta gidajen rediyo, talabijin da kuma shugabannin al’umma kan hanyoyin kare kai daga cutar.

 

 

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending