News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Satar Wayar Hannu Guda 41 A Maiduguri
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta ce ta kama wani mutum, Baba Isa Yerima, bisa zargin hannu a satar wayoyin hannu guda 41 a Maiduguri, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga Agusta, 2026, bayan amfani da na’urar bibiyar wuri (Tracker) wajen gano wasu wayoyin Samsung da iPhone da aka bayar da rahoton ɓacewarsu.
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Bai Wa Ɗalibai Kyautar DATA Kullum
Ya ce jami’an rundunar Crack Squad sun bi sawun wayoyin zuwa gidan wanda ake zargin da ke yankin Kwanan Yobe a Maiduguri, inda suka gudanar da bincike tare da ƙwato wayoyi 39.
A cewar rundunar, an riga an gano wasu wayoyi biyu, lamarin da ya sa adadin wayoyin da aka gano ya kai 41, waɗanda aka kiyasta ƙimarsu da kusan Naira miliyan 25.
Rundunar ta ce wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da kuma ƙoƙarin gano wasu mutanen da ake zargin suna da hannu a lamarin.
ASP Daso ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
