News
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar dubiya ne da kuma ganin yadda su kansu ma’aikatan asibitin suke kulawa da lafiyar al’ummar jihar Kano.
Ziyarar ta Gwamnan ta kasance ne a ranar juma’a cikin dare, a Irin bazatan da ya saba yi zuwa asibitocin gwamnati domin ganin yadda ake kulawa da lafiyar al’umma a wannan lokacin.
Bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya gama duba mara sa lafiya, kuma ya kewaye kowanne ɓangare na asibitin tare da rakiyar likitan dake kan aiki tare da ma’aikatansa a wannan daren.
Gwamnan kuma ya yaba da yadda yaga ma’aikatan wannan asibiti kwararru na Best Choice suke gudanar da ayyukan su na kula da lafiyar al’ummar jihar Kano.
Wannan ta nuna karara gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ba wai iya abin da ya shafi mallakin gwamnati yake mayar da hankali a kai ba, har da abin da ya Shafi na ƴan kasuwa na al’ummar jihar, suma ya na basu mahimmanci domin cigaban jihar Kano baki daya.
A yayin ziyarar Gwamna ya godewa shuwagabannin asibitin kwararru na Best Choice da ma’aikatan su, ganin yadda ya same su cikin dare kamar rana suna gabatar da ayyukan ceton rayukan al’umma. Sannan Gwamnan ya bawa Ma’aikatan kyauta ta musamman domin karin kwarin gwuiwar gudanar da ayyukan su.
Asibitin kwararru na Best Choice Specialist na nan a Tal’udu junction daura da makarantar Sheikh Al Rayyan da ke Kano, kuma suna gudanar da ayyukan cikin awanni 24/7 tare da kwararrun likitoci da ma’aikata a kowane sashe
