Connect with us

News

Atiku Ya Maka Shugaba Tinubu A Kotu Saboda Zargin Gabatar Da Takardun Bogi

Published

on

Tinubu Ya Cutar da Al’ummar Rivers Ta Hanyar Ƙaƙaba Dokar Ta ɓaci — Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ruga kotu domin hana shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tsayawa takarar zaɓe mai zuwa, saboda abinda ya kira gabatar da takardun bogi ga hukumar zaɓe.

Atiku wanda da kan sa ya jagoranci tawagar lauyoyin sa zuwa kotu a Abuja, ya buƙace ta da ta tantance takardun takarar da shugaba Tinubu ya gabatar na tsayawa takarar shekarar 2023 da 2027 domin sanin banbancin mai ɗauke da sunan Bola Ahmed Tinubu da kuma Bola Adekunle Tinubu.

Babbar Mai Shari’a Ta Jihar Kano Ta Saki Fursunoni Bakwai Saboda Rashin Lafiya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar yace saboda girmar matsalar ta sa da kan sa ya yi tattaki zuwa kotun domin rantsuwa da kuma gabatar da ƙara dan ganin an yi amfani da doka wajen mutunta kundin tsarin mulkin ƙasa, ba tare da bada fifiko tsakanin wasu ƴan Najeriya ba.

Ƙarar ta kuma nuna cewar takardar shaidar kammala bautar ƙasar da Tinubu ya gabatar ya saɓa da takardar shaidar kammala karatun sa.

Atiku ya kuma buƙaci hukumar zaɓe ta gabatar da fom mai lamba CF001 da Tinubu ya gabatar domin zaɓen shekarar 2023 da 2027 wanda ya nema a bashi kafin gabatar da ƙarar amma aka hana shi.

Advertisement

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba sa buƙatar ƴan Najeriya su yanke hukunci a kafofin sada zumunta, ko kuma INEC ta yanke hukunci a kan lamarin, saboda haka suka je kotu wadda ke da hurumin gabatar da hukunci kan lamarin.

Atiku ya ce idan kuwa babu banbanci tsakanin Tinubu Bola Adekunle da Bola Ahmed Tinubu, to kotu ce kawai ke da hurumin tabbatar da haka.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce babu wanda ya fi ƙarfin doka tsakanin shi da Tinubu da kuma shugaban Najeriya, saboda haka wannan matsala ce da ta shafi kundin tsarin mulki.

 

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending