News
Sarkin Shanu Ya Shirya Babban Shagalin Maulidin Fiyayyen Halitta A Kano
Sarkin Shanu, Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Yusuna, ya gayyaci al’umma zuwa shagalin Maulidin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad , da za a gudanar a Kano.
A cikin sanarwar gayyatar da ya fitar, Dr. Abubakar Yusuna ya ce an shirya shagalin ne domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad , tare da bayyana muhimmancin koyi da kyawawan ɗabi’u da koyarwar Manzon Allah.
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
Sanarwar ta ce za a fara gudanar da shagalin ne daga ranar Juma’a, 1 ga watan Rabi’ul Awwal, wanda zai ci gaba har izuwa 30 ga watan Rabi’ul Awwal.
Za a gudanar da babban taron ne a Kurna Babballayi, Naira da Kwabo, a Fadar Sarkin Shaun, inda ake sa ran samun halartar ɗimbin al’umma.
Sarkin ya yi kira ga ‘yan uwa, abokan arziki da sauran al’umma da su halarci shagalin domin tunawa da rayuwar Annabi Muhammad ﷺ da kuma ƙara ƙaunar Manzon Allah a zukatan Musulmi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba wa al’umma damar halartar taron cikin aminci, Ya sanya albarka a cikinsa, tare da karɓar dukkan ayyukan alheri da za a gudanar.
“Allah Ubangiji Ya ba mu ikon halarta. Amin Ya Rabbal Alamin,” in ji sanarwar.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
