News
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu (MATFDAT), Alhaji Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa babu wani mutum ko wata hukuma da za a yi wa rangwame a yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi a jihar.
Muhyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wani shirin DuniyarMu a Yau, wanda Freedom Radio Kano, inda ya ce duk wanda aka samu yana safarar, sayarwa ko aikata wani laifi da ya shafi miyagun ƙwayoyi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
Ya ce rundunar ta riga ta kai wasu daga cikin waɗanda suka kamu da shan miyagun ƙwayoyi zuwa Cibiyar Gyaran Hali ta Kiru, domin ba su kulawa da kuma taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.
Haka kuma, ya bayyana cewa an gurfanar da wasu waɗanda ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi a gaban kotu, yayin da aka rufe wasu shagunan sayar da magunguna saboda karya ƙa’idojin da suka shafi sayarwa, adanawa da sarrafa magunguna.
“Babu wanda zai tsira. Duk wanda ke sayarwa ko amfani da miyagun ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu. Babu mafaka ga masu aikata irin wannan laifi a Kano,” in ji shi.
Shugaban rundunar ya ce za a ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da malaman addini, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula, ’yan kasuwa, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tunkarar matsalar ta hanyar haɗin gwiwa.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
