Connect with us

News

ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi

Published

on

Femi Gbajabiamila

Hukumar ICPC ta ce ba ta samu wata hujja da ke nuna cewa Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatar fadar shugaban ƙasa, ya aikata laifi a cikin badakalar wata hukumar gwamnati ta bogi ba.

Hukumar ta ce mutumin da ya yi ikirarin cewa shi ne darakta janar na Presidential Foreign Investment Promotion Council, Prince Adeniyi Adeyemi, ba gwamnatin tarayya ta naɗa shi ba, kuma takardar naɗin da ya gabatar ta kasance jabun takarda ce.

Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa

ICPC ta kuma ce hukumar da Adeyemi ke ikirarin jagoranta ba a taɓa kafa ta da wata doka ko umarnin gwamnati ba.

Shugaban ICPC, Musa Aliyu, ya ce Adeyemi ya kafa wasu hukumomin bogi guda biyu, tare da amfani da wasu takardu na bogi domin ya ba wa ayyukansa kamannin halattacciyar hukumar gwamnati.

Ya ce mutumin ya kuma kutsa cikin ofisoshin tsohuwar Presidential Economic Advisory Council, inda ya yi amfani da wurin wajen gudanar da ayyukansa.

Advertisement

Hukumar ta ce bincikenta bai gano cewa an amince ko an fitar da kuɗin gwamnatin tarayya zuwa hukumar bogin ba.

 

 

 

VANGUARD

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending