Connect with us

News

Mutane Sun Nitse A Ruwa A Kokarin Tserewa Harin Yan Bindiga A Sokoto

Published

on

Ana fargabar akalla mutum 21 sun rasa rayukansu yayin da wasu 37 su ka shiga hannun ƴan bindiga bayan wani mummunan hari da su ka kai garin Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Rahotanni sun ce harin ya fara ne da misalin karfe 9 na dare ranar Litinin ya ci gaba har zuwa wayewar garin Talata. Maharan sun kashe mutane, sun ƙona gidaje biyu, sun sace dabbobi tare da tilasta dubban mazauna yankin tserewa daga gidajensu.

Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa

Sannan mutane da dama sun nutse a kogi yayin da su ke kokarin tserewa harin, bayan kwale-kwalen da su ke ciki sun kife. Sai dai an ceto mutum bakwai da ransu, yayin da ake fargabar wasu 18 sun mutu a ruwa.

Mazauna yankin sun ce mafi yawan waɗanda a ka sace mata ne da ƙananan yara ne, tare da zargin jami’an tsaro da rashin kai ɗauki duk da cewa an sanar da su tun kafin maharan su kammala harin.

Harin na zuwa ne mako guda bayan wani makamancin hari da a ka kai a yanki, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum takwas, lamarin da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a ƙaramar hukumar Sabon Birni.

Advertisement

Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni Ayuba Hashimu da kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Sokoto Ahmad Rufai sun tabbatar da faruwar harin. Rundunar ƴan sanda ta ce an tura karin jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya da hana sake aukuwar irin wannan hari a yankin.

 

 

The Guardian

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending