Connect with us

News

TINUBU DA SHETTIMA BA SA NAJERIYA — “Ba Ni Ne Mukaddashin Shugaban Ƙasa Ba” — Akpabio

Published

on

Akpabio 1 768x512 (1)

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce ba shi ne mukaddashin shugaban Najeriya ba, duk da kasancewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, a halin yanzu ba sa cikin ƙasar.

Akpabio ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Ikot Ekpene, Jihar Akwa Ibom, inda ya ce Shugaba Tinubu na ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati daga Turai, yayin da yake hutun aiki.

Yan Siyasar Sun Karkatar Da Naira Biliyan 360 Daga Lalitar Gwamnati Sun Sayi Kadarori A Amurka — Rahoto

Sanata Akpabio ya ce babu wani gibi a kujerar shugaban ƙasa, yana mai jaddada cewa kasancewar Tinubu a ƙasashen waje ba yana nufin ya daina gudanar da ayyukan ofishinsa ba.

Maganar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan wanda ke amfani da ikon shugaban ƙasa, bayan Tinubu da Shettima sun kasance a ƙasashen waje a lokaci guda.

Kakakin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya yi tambaya kan wanda ke kula da harkokin ƙasar bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, musamman Sashe na 145 da ya yi tanadin yadda ake mika wasu daga cikin ayyukan shugaban ƙasa idan ya kasance ba ya iya gudanar da su.

Advertisement

Haka kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi kira da a bayyana wa ’yan Najeriya wanda ke amfani da ikon shugaban ƙasa a lokacin da Tinubu da Shettima ba sa ƙasar.

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu na ci gaba da gudanar da harkokin ƙasar daga Turai, inda aka sanar cewa ya tsawaita hutun aikinsa da wasu ’yan kwanaki, kuma ana sa ran zai koma Najeriya a ƙarshen mako.

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending