News
KANO: Kwamitin Yaƙi Da Shaye-shaye Ya Ƙwato Kwayoyin Pregabalin Miliyan 3.18

Kwamitin kar ta kwana na yaƙi da shaye-shaye da daba a Kano ya kama mutum ɗaya tare da ƙwato ƙwayoyin maganin Pregabalin da ake zargin na miyagun ƙwayoyi ne kimanin miliyan 3.18 a yankin Sabon Gari da ke Kano.
Hukumar ta ce ta kama mutumin mai suna Gregory Ogbuji, mai shekaru 34, a wani samame da ta kai wani gida da ke lamba 13, Apple Avenue, Normansland, Sabon Gari, cikin ƙaramar hukumar Fagge.
A wata sanarwa da sakataren kwamitin yaɗa labarai na hukumar, Lamara Garba, ya fitar, ya ce samamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri ta hanyar hanyoyin sadarwar hukumar.
Ya ce kamen ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da rundunar ɗaukar matakin gaggawa domin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.
Sanarwar ta ce an gurfanar da wanda ake zargin bisa sashe na 249 na dokar Penal Code, yayin da wani mutum da ake zargin yana da alaƙa da lamarin ya tsere.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana nasarar a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin farko da rundunar ta samu, yana mai cewa kusan takwas cikin mutane 10 da ake kama wa a ayyukan yaƙi da miyagun ƙwayoyi na da alaƙa da shan kwayar Pregabalin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani motsi da suke zargin yana da alaƙa da fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a jihar..
-
News6 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News3 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News6 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
