News
Dakarun Soji Sun Hallaka Masu Garkuwa Da Mutane, Sun Ƙwato Harsasai 5,163 A Kogi

Dakarun Rundunar Sojojin Nijeriya ta Brigade ta 12 sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato harsasai 5,163 da bindigogin AK-47 guda biyu a wani samame da suka kai a Jihar Kogi.
Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Brigade ta 12, Laftanar Hassan Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
’Yan Sanda Sun Gargaɗi ’Yan Siyasa Kan Lalata Kayan Kamfen Abokan Hamayyarsu Gabanin Zaɓen 2027
Ya ce dakarun sun gudanar da samamen ne a ranar 3 ga Nuwamba, 2026, a dajin Edimogbo da ke Ƙaramar Hukumar Igalamela/Odolu, bayan wani artabu da suka yi da waɗanda ake zargin a maɓoyarsu ranar 2 ga watan.
A cewarsa, aikin ya mayar da hankali ne kan bin sawun waɗanda suka tsere bayan artabun, da kuma binciken sauran wuraren da ake zargin masu garkuwar ke amfani da su a matsayin maboyarsu.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda biyu, ƙunshin harsasai bakwai, harsasai 438 na nau’in 7.62mm x 54 da kuma harsasai 4,725 na musamman na 7.62mm.
Haka kuma, sojojin sun ƙwato wayoyin hannu guda biyu da na’urar cajin waya (power bank) guda ɗaya.
Rundunar ta ce wannan nasara wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na murƙushe ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a Jihar Kogi.
Ta ƙara da cewa za ta ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.
-
News4 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News4 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
