Opinion
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
Daga Abba Anwar
Kamar yadda jihar Legas ke alfahari da kammala ayyuka 377 a cikin shekaru uku, da kammala Layin Jirgin Kasa na Red Line Mataki na 1 da sauran ayyukan da ake ci gaba da su. Kamar yadda jihar Abia ke alfahari da kammala ayyuka 76 tare da 36 da ake yi, da manyan ayyuka na gina sama da kilomita 600 na hanyoyi, gyaran hanyar Port Harcourt, gyaran Cibiyoyin Lafiya na Farko 277, 135 daga cikinsu na aiki, da gyaran hedkwatar Kananan Hukumomi 17. Haka nan jihar Kano na alfahari da kammala ayyuka 799, yayin da ayyuka 709 ke a matakai daban-daban na kammalawa.
Idan jihar Katsina ta kammala ayyuka 89 daga cikin ayyuka 114 da aka tsara, ciki har da hanyoyin cikin gari 23, cibiyoyin lafiya 15 da ke da na’urar hasken rana, da dakunan ajin karatu 28. Idan kuma jihar Gombe ta kammala ayyuka 74 daga cikin 111, da suka hada da gina hanyoyi 19, cibiyoyin lafiya 11, da gyaran makarantu 25. Sannan jihar Niger ta kammala ayyuka 25 na gina kilomita 5 na hanya a kowace karamar hukuma 25, tare da gina cibiyoyin lafiya 100 na Mataki na 2 da ayyukan birnin da suka kai kashi 30 cikin 100 na kammalawa. To jihar Kano, ban da ayyuka 799 da aka ambata a sama, Gwamna Abba Kabir Yusuf yana da ayyukan ci gaba sama da 1,508 a fadin Kananan Hukumomi 44.
Wasu jihohin kamar Bauchi sun kammala ayyuka 61 daga cikin 108 da aka yi niyya, ciki har da hanyoyin cikin gari 12, manyan Asibitoci 9 da rijiyoyin burtsatse 22. Ayyukan ci gaba na jihar Delta sun hada da kammala babbar hanyar Emu-Obodeti-Abbi-Abraka mai tsawon kilomita 32.5 da gyaran hanyoyin kananan hukumomi, tare da fara gina gadoji biyu. Jihar Oyo kuwa ta kammala hanyar Iseyin-Okeho da Mataki na 1 na cibiyoyin lafiya 200, tare da babban aikin gina hanyar Shaki-Okerete mai darajar Naira Bilyan 144 da ake ci gaba da shi. Duk da wadannan kokarin na jihohin, jihar Kano na nan gaba da su ta yi musu fintinkau!
Bisa bayanan da ake iya samu ga jama’a, kamar yadda muka nuna a sama, jihar Benue ta kammala ayyuka 50 na hanyoyin cikin gari, gyaran Sakatariyar Gwamnati da Majalisar Dokokin Jihar, tare da ayyuka 100 da ake yi. Jihar Akwa-Ibom kuma ta kammala gina hanyoyi sama da kilomita 1,300 a fadin jihar, da sauran manyan ayyuka kamar filin wasa na Akpan Andem Market, makarantu, da babbar hanyar Ikot Esu-Otomo-Azumini mai tsawon kilomita 15.13km. Jihar Anambra kuma ta kammala ayyukan hanyoyi mai tsawon kilomita 15.62km a Okpoko da Beltway da ke hada birane 4, tare da manyan ayyukan da ake yi na hanyar Amawbia-Ekwulobia da kashi 80 cikin 100 na kammala hanyar Awkuzu-Igbariam mai tsawon kilomita 19.1km.
Bisa bayanan da Kwamishinan Ma’aikatar Public Procurement Monitoring and Evaluation, Nura Ma’aji Sumaila, ya bayyana kwanan nan a wani taron manema labarai, ya nuna cewa Ayyukan sabunta birane suna da kudin kwangila na Naira Biliyan Dari da Sittin da Tara (Naira Biliyan 169) da kuma aikin gina hanyoyin kilomita 5 a Kananan Hukumomi 38 da kudin kwangila na sama da Naira Biliyan Dari da Sha Takwas (₦118B).
Ya kara da cewa, “Akwai Ayyukan Inganta Tsaro ta hanyar ba da kwangilar gina ofisoshin tsaron unguwannin jihar Kano a Kananan Hukumomi 36, da kudin kwangila na sama da Naira Bilyan Shida da Milyan Dari Takwas da Sittin da Uku (₦6.863B). Wannan na nuna ci gaba da gwamnati ke yi wajen zuba jari a harkokin tsaro da ababen more rayuwa.
Haka kuma akwai ayyukan ababen more rayuwa na karkara a fadin Kananan Hukumomi 44, wadanda suka hada da ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da sauran ayyukan jin dadin jama’a, da kudin kwangila na sama da Naira Biliyan Dari Uku da Casa’in da Bakwai (₦397B). Wadannan ayyuka na tallafawa daidaiton ci gaba da inganta hidima a yankunan karkara.”
Sauran ayyukan kuwa, a cewarsa, suna da jimillar kudin kwangila na Naira Biliyan Dari Biyu da Hamsin da Biyar (N255B).
Da ka karanta jihohin da na bayar a sama, za ka fahimci cewa, na taba dukkanin yankuna 6 na kasar nan. Ba kawai na zabi jihohi biyu a kowane yanki ba, na zabi jihohin da suka fi yin aiki a yankunansu. Shi ya sa na ce, Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kuɗi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35.
Abin da ya sa Kano ta zarce sauran jihohi 35 na kasar nan, ba kawai wajen kammala ayyukan da suka shafi jama’a ba ne, har ma da tsarin kulawa da kimantawa na gaskiya wanda daga karshe ya kai ga biyan ‘yan kwangila. Abin lura ne cewa, daga cikin Naira Biliyan Dari Tara da Ashirin da Takwas (N928B), jihar ta iya biyan sama da Naira Biliyan Shida Dari (N600B).
Wato an biya kashi 64.7 cikin 100. Wato an biya kusan kashi biyu cikin uku. Sauran kuma suna kan hanyar biya. Wannan nasara ce ba wai a Najeriya kadai ba, har ma a fadin yankinmu. Babu wata hanya biyu game da haka. Ba wai ba inke!
Ga masu kishin ci gaba, tsarin gudanar da ayyuka, tun daga tsarawa, lokacin aiwatarwa da bayan kammalawa, har zuwa lokacin biyan kudi, dalili ne da ya isa ya sa a sake zaben Gwamna Yusuf a 2027. Zamansa a matsayin Kwamishinan Ayyuka shekaru da dama da suka gabata da sauran mukamai na gwamnati, sun ba shi damar fahimtar yadda ake tsarawa, aiwatarwa, kulawa, kimantawa da biyan ayyuka.
Na yarda da Kwamishina Sumaila lokacin da ya yabi Gwamna da gwamnati kan “… niyyar gwamnati na tabbatar da rarraba ayyuka a birane da karkara, tare da jaddada samun darajar kudi, ingancin aiki, da tasirin da za a iya gani a rayuwar al’umma. Yawan ayyukan ya yi daidai da abubuwan da gwamnatin jihar ta ba da fifiko, ciki har da hanyoyi, sabunta birane, kayan aiki, sufuri, tsaro da ayyukan jin dadin jama’a.”
Ranar da Gwamna Yusuf ya kafa wannan Ma’aikata ta Kayan Aikin Gwamnati, Kulawa da Kimanta Ayyuka kuma ya nada Nura Ma’aji a matsayin Kwamishinan farko, wanda na san shi sama da shekaru 25, a matsayin mai fafutukar kare hakkin bil’adama da inganta gaskiya da yin abu ba rufa-rufa, tun ma kafin a kafa a samar da shirin nan na Open Government Partnership (OGP), na san Gwamnan na da niyyar gudanar da mulki nagari.
Tare da Sumaila, ina da kwarin gwiwa cewa, niyyar Ma’aikatar ta taka muhimmiyar rawa “… wajen kare dukiyar jama’a, karfafa tattalin arzikin jihar, inganta zirga-zirga, tallafawa tsaro a al’umma, da kuma cimma hakan ta hanyar samar da cigaba mai ma’ana, kulawar ayyuka da samar da abubuwan gudanar da aikin gwamnati ta hanya mai gaskiya.”
A wannan taron manema labarai na dauki kudurin Kwamishina Sumaila da muhimmanci lokacin da ya ce, “Ma’aikatar Kayan Aikin Gwamnati, Kulawa da Kimanta Ayyuka ta himmatu wajen tabbatar da samun darajar kudi da ingantacciyar isar da ayyuka ta hanyar ingantacciyar kulawa da dukkan burin al’umma.”
Yana da muhimmanci a lura cewa, manyan ayyukan da aka kammala a Kano sun hada da, ba wai kawai, hanyoyin birni 40, cibiyoyin lafiya 44, makarantu 120 da wuraren samar da ruwa ga al’umma 5. Ba tare da an manta da sake farfado da tsarin birnin Kano na asali ba don ya dace da zamani da kyautata shi.
Daga cikin ayyuka 709 da ke kan hanyar kammalawa akwai manyan gadojin mu na Dan Agundi da Tal’udu. Wadanda suka kai sama da kashi 80 cikin 100 na kammalawa. Matsayin da aka sanya wadannan gadoji, na rage cunkoso, sake tsarawa, kyautatawa da sake gina Kano a matsayin birni na karni na 21 na nuna yadda Gwamna Yusuf ke da zurfin tunani wajen mulki da isar da sakamako.
Da kallon wannan Gwamna mai kishin jama’a, za ka fahimci cewa, wannan mutum yana da karfin niyya, cikakken fahimtar bukatun mutanen Kano kuma yana da dukkanin kudurin da ake bukata don yin wa jama’a hidima da gaskiya. Wannan da sauran dalilai ne suka kara ba ni kwarin gwiwa na tunanin cewa ba za a samu cikas ba a kan hanyar Maigirma Gwamna Yusuf, a zaben da ke tafe, na 2027. Kullum kofofin nasara ne ke kara budewa da kuma tabbatuwa.
Anwar ya rubuto daga Kano
Asabar, 18 ga Yuli, 2026
