Politics
Kanawa Sun Yarda Da Tsarin NDC Kwankwasiyya’ — Hon. Sagir Wada Sinkin
Dan takarar Majalisar Jiha a Karamar Hukumar Tarauni, Hon. Sagir Wada Sinkin Mai Iyali, ya bayyana godiyarsa ga al’ummar Jihar Kano bisa yadda suke ci gaba da nuna goyon baya da amincewa da tsarin jam’iyyar NDC Kwankwasiyya da kuma ‘yan takararta masu kishin kasa.
Hon. Sagir Wada Sinkin ya ce al’ummar Kano sun nuna cikakken goyon baya ga manufofin jam’iyyar tare da amincewa da shugabannin da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma jagoran siyasa, Peter Obi.
“An Mayar Da Siyasa Fagen Cin Mutunci A Najeriya” — Sheikh Daurawa
Ya bayyana hakan ne yayin da yake gode wa magoya baya da ‘ya’yan jam’iyyar bisa halartar taron da suka gudanar zuwa gidan jagora domin tattauna hanyoyin cigaban tafiyar Kwankwasiyya da karfafa hadin kai a tsakanin mabiyanta.
“A madadinmu, muna mika godiya ta musamman ga daukacin al’ummar Kano bisa yadda suke ci gaba da yarda da tsarinmu da kuma fitowa domin tallafawa tafiyar NDC Kwankwasiyya,” in ji shi.
Hon. Sagir Wada Sinkin ya kuma yi kira ga magoya baya da su ci gaba da hada kai tare da mara wa jam’iyyar baya domin tabbatar da cigaba da nasarar manufofin da suka sanya gaba.
Ya jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya na ci gaba da samun karbuwa ne saboda manufofinta na kishin kasa da kokarin inganta rayuwar al’umma.
