News
Bai Kamata Ace Gwamnoni Su Rika Tare Wa A Jihohin Da Ba Nasu Ba Lokacin Zabe —Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnoni da manyan ‘yansiyasa da jami’an gwamnati ke tarewa a jihar da ake zaben gwamna, yana mai cewa hakan na iya zama ƙalubale da matsin-lamba kan sahihancin zaɓuka da tasirin sauran jam’iyyu.
Jonathan ya yi wannan kalamai ne bayan da a makon jiya aka gudanar da zaɓen gwamna a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Nijeriya, da kuma a watannin baya a jihihin Ekiti da Ondo, inda aka ga irin wannan lamari na dandazon ‘yansiyasa da jami’an tsaro.
Tsokacin na Jonathan ya zo ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, inda ya jinjina wa hukumar zaɓen Nijeriya da jami’an tsaro da al’ummar jihar Osun kan yadda zaɓen ya gudana, wanda gwamna mai ci, Ademola Adeleke na jamiyyar adawa ta Accord ya lashe.
“Yayin da muke yaba wa tsarin zaɓen kansa, akwai wasu batutuwa da suka dabaibaye zaen, kuɓma, mafi muhimmanci shi ne, wani sabon salo da ke kunno kai game da yanayin siyasa a lokutan zaɓukan da ba na gama-gari ba wanda ke tada hankali,” in ji Jonathan.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi karatun bayan inda ya ambato irin wannan lamarin da ya faru lokacin da yake kan mulki a matsayin shugaban ƙasa, irin wannan yanayi ya taɓa faruwa a yayin zaɓukan gwamna na Anambra a shekarar 2013 da na Ekiti a shekarar 2014, inda manyan shugabannin siyasa suka tattara magoya baya tare da yin cincirindo a jihohin.
“Bayan an yi mini bayani dalla-dalla, na umarci shugabannin jam’iyya da manyan jami’an gwamnati da su fice daga jihohin nan take,” in ji shi.
Jonathan ya bayyana wannan al’amari a matsayin mara kyau, inda ya ce idan ba a shawo kansa ba, yana iya zama barazana ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya tare da haifar da mummunan tasiri na dogon lokaci ga dorewar dimokuradiyya.
