News
KADUNA: Malamai Sama Da 200 Sun Yi Murabus Daga Aiki A Jami’ar KASU
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ce sama da malamai 200 sun bar aikin jami’ar saboda rashin kyawun yanayin aiki da kuma gazawar aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da kungiyar a shekarar 2025.
Shugaban ASUU na reshen KASU, Dr Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Kaduna.
Gwamnatin Kano Ta Haramta Wa Masu “Chemists” Yin Karin Ruwa Da Karin Jini
Ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar na kara jefa malaman jami’ar cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka bar aikin.
Saboda haka, kungiyar ta bai wa mahukuntan jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin makonni biyu da su fara aiwatar da yarjejeniyar tare da tabbatar da an yi aiki da tanade-tanadenta a jami’ar.
ASUU ta kuma gargadi mahukuntan jami’ar cewa, idan ba a dauki matakan da suka dace cikin wa’adin da ta kayyade ba, za ta shiga yajin aikin gama-gari da ta ce zai kasance mai tsauri kuma na sai baba-ta-gani.
