Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke Kwayoyin Tramadol Sama Da 370,000 A Motar  ‘Luxurious’ Da Ke Kan Hanyar Zuwa Kano

Published

on

1786980729542

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke sama da kwayoyin Tramadol 370,000 da aka yi safarar su zuwa Jihar Kano a cikin wata motar kamfanin Ezenwata.

Majiyarmu ta bayyana cewa jami’an NDLEA sun gano kwayoyin ne a cikin wata motar haya kirar ‘Luxurious’ da ke dauke da nau’o’in miyagun kwayoyi daban-daban.

Gwamnatin Kano Ta Musanta Zargi Ware N235.4m Domin Gina Makarantar Da Ba Ta Wanzu Ba A Sumaila

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa an boye wasu daga cikin kwayoyin ne a cikin motar domin kauce wa jami’an tsaro yayin safarar su zuwa Kano.

Haka kuma, an ce daya daga cikin wadanda ake zargin ya bar garinsu zuwa Zaria, Jihar Kaduna, domin gudanar da harkar dillancin miyagun kwayoyi.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa jami’an NDLEA sun kama wadanda ake zargin tare da kwayoyin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a safarar miyagun kwayoyin.

Advertisement

Hukumar NDLEA ta sha nanata cewa za ta ci gaba da daukar matakan dakile safarar miyagun kwayoyi da kuma gurfanar da wadanda ake samu da hannu a harkar gaban kuliya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending