News
Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan sakamakon gwajin lafiya da ya tabbatar wata mata guda ɗaya tana ɗauke da ƙwayoyin cutar.
Ministan Lafiya na ƙasar, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026.
KANO: An Kama Wani Matashi Kan Zargin Buga Takardun Indigene Na Bogi A Karamar Hukumar Dala
Ya ce tuni an killace matar a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja inda take samun kulawar likitoci.
Ministan ya ce matar ta shigo Najeriya ce daga Uganda ta jirgin sama, kuma an fara binciken waɗanda suka yi mu’amala da ita, inda aka gano mutum 44 da yanzu haka ana sa ido a kansu domin hana yaɗuwar cutar.
Hukumomin lafiya sun kuma ƙara sa ido tare da ɗaukar matakan ƙarfafa kariya daga yaɗuwar cutar a asibitin da ake jinyar matar.
Gwamnatin ta buƙaci asibitocin gwamnati da masu zaman kansu a faɗin ƙasar su ƙara sanya ido, su killace duk wanda ake zargin ya kamu da cutar, tare da kai rahoton duk wata alama ga hukumomin lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ita ce ƙasa ta farko a Yammacin Afirka da ta tabbatar da ɓullar cutar da ke da alaƙa da annobar Ebola da aka ayyana a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da Uganda a watan Mayu.
Kazalika, wasu bayanai a wannan Talatar sun nuna cewa Kenya ta samu mutane tara da suka kamu da cutar, a cewar ma’aikatar lafiyar ƙasar.
Kawo yanzu dai Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na ci gaba da kasancewa cibiyar wannan annoba, inda aka samu sama da mutane 9,400 da suka kamu da cutar da kuma fiye da mutum 4,500 da suka mutu zuwa tsakiyar watan Oktoba.
-
News5 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News3 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

