Connect with us

News

HAWAN DABA DA KILISA :Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Za Ta Lamunci Kalaman Tada Zaune Tsaye Ba

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi sarakunan gargajiya, shugabannin addini da na al’umma, ’yan siyasa da sauran jama’a da su guji kalaman da za su iya haifar da rashin bin doka, tada zaune tsaye ko jefa al’umma cikin rikici.

Gargadin na zuwa ne musamman kan matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na takaita wasu ayyukan hawan daba da ake shirin gudanarwa da kuma kilisa a cikin birnin Kano har sai abin da hali ya yi.

An Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 80 A Cikin Mako Biyu A Arewacin Nijeriya — Rahoto 

Mai Bai wa Gwamnan Kano Shawara kan Harkokin Shari’a da  Kundin Tsarin Mulki, Aminu Hussaini, ne ya fitar da sanarwar bayan wani bidiyo na Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’Agundi, ya yaɗu a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon, Sarkin Dawaki Babba ya bayyana ra’ayinsa kan matakin da gwamnati ta ɗauka na takaita ayyukan hawan daba da kuma kilisa, tare da bayyana fahimtarsa kan shari’ar da ake yi dangane da masarautar Kano.

Sai dai gwamnatin ta ce duk da cewa ɗan ƙasa na da ’yancin bayyana ra’ayinsa kan al’amuran da suka shafi jama’a, amma aiwatar da umarnin kotu al’amari ne da ya rataya a kan kotuna.

Advertisement

A cewar sanarwar, fahimtar mutum kan wani umarnin kotu da ke aiki ba ta ba shi damar yin watsi da umarnin da wata hukuma mai iko ta bayar.

“Idan wani mutum na ganin cewa umarnin gwamnati ya saɓa wa umarnin kotu, hanyar da ta dace ita ce neman ƙarin haske daga kotu ko kuma ɗaukar matakin shari’a da ya dace, maimakon bayyana aniyar yin watsi da umarnin ko ƙarfafa wasu su yi hakan,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini da na al’umma, ’yan siyasa da sauran jama’a da su nuna kamewa, tare da tabbatar da cewa kalamansu da ayyukansu ba su ƙarfafa rashin bin doka, faɗa ko tada hankalin jama’a ba.

Ta ce ya kamata a bar shari’ar da ke gudana kan masarautar Kano ta kammala ba tare da an riga an yanke hukunci ko kuma an yi amfani da ita wajen haifar da rikici tsakanin jama’a da hukumomin gwamnati ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa rashin amincewa da matakin gwamnati na iya bayyana, amma ya kamata a bi hanyoyin da doka ta tanada wajen gabatar da koke-koke.

“Umarnin da doka ta tanada zai ci gaba da aiki har sai wata hukuma mai iko ta soke shi, dakatar da shi ko ta sauya shi,” in ji sanarwar.

Advertisement

Gwamnatin ta ce ba za ta bari wani mutum ko ƙungiya ta mayar da wata takaddama ta halal zuwa kalubale ga zaman lafiyar jama’a ba.

Ta ce matakin takaita ayyukan an ɗauke shi ne a matsayin rigakafi domin hana yiwuwar tashin hankali, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma tabbatar da zaman lafiya da doka da oda.

Haka kuma, gwamnatin ta umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da aiwatar da matakin, tare da ɗaukar matakan da suka dace bisa doka kan duk wanda ya karya dokar da aka saka ko kuma ya aikata abin da zai iya barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending