Connect with us

News

Wasu Ɓatagari Ɗauke Da Makamai Sun  Farmaki Ayarin Kwankwaso Da Aminu Gwarzo A Bichi

Published

on

FB IMG 1794770557857
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

An samu ɓarkewar rikici a ƙaramar hukumar Bichi bayan da wasu ɓatagari ɗauke da makamai suka kai hari kan ayarin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Lamarin ya faru ne yayin da tawagar ke zagayen neman goyon bayan al’umma, bayan ta kammala taruka a ƙananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai.

Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto

Da yake tabbatar da faruwar harin, mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan na NDC, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu, ya bayyana cewa tun a kan hanyarsu ta shiga Bichi suka fara samun bayanan sirri cewa an tare hanya domin hana su gudanar da gangamin.

A cewarsa, da isarsu garin sun tarar da alamun jefe-jefe, kuma jim kaɗan bayan sun wuce sakatariyar ƙaramar hukumar ne wasu gungun matasa ɗauke da muggan makamai suka fito suka far wa ayarin nasu.

Kwamared Shu’aibu ya ƙara da cewa harin ya yi sanadin jikkatar wasu daga cikin magoya bayansu tare da lalata ababen hawa, yana mai shaida cewa ya ga motoci kusan bakwai da aka farfasa a wurin.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending