News
An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya — Rundunar Ƴansanda

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta bayyana cewa an kashe mutane 418, yayin da aka yi garkuwa da wasu 227 a sassa daban-daban na ƙasar cikin watanni biyu da suka gabata.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton ayyukanta na tsaro da aka fitar a watan Nuwambar 2026, inda ta ce ta samu rahotannin hare-haren ’yan bindiga guda 168 da ayyukan ta’addanci 51 a cikin makonni takwas.
Rahoton ya kuma nuna cewa an samu rahotannin fashi da makami guda 165, rikicin ƙungiyoyin asiri 73, da kuma laifukan cin zarafin mata da suka shafi jinsi guda 49 a tsawon lokacin.
Haka kuma, rundunar ta ce ta kama mutum 1,519 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ƙwato bindigogi 191 da alburusai 3,873. Ta kuma ƙwace motoci 117 da aka sace ko kuma ake amfani da su wajen aikata laifuka.
A wani ɓangare na ayyukan tsaron, rahoton ya ce jami’an tsaro sun ceto mutane 255 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe wasu mutane 56 da ake zargin ’yan bindiga ne yayin samamen da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.
