Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Wata ‘Yar Kasar Uganda Da Ta Boye Koken Dauri 87 A Cikin wandonta

Published

on

IMG 20261109 190733 079
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar NDLEA da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya ta ce ta kama wata ’yar ƙasar Uganda, Farida Nansubuga a filin jirgin saman Murtala Muhammed bisa zargin ɓoye ɗauri 87 na koken a wandonta a yayin da take yunƙurin tafiya da ita ƙasarta.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi, ta ce an kama matar da koken mai nauyin kilogiram 1.15 a ranar 3 ga watan Nuwamba a yayin da take shirin shiga jirgi zuwa Uganda.

Wasu Bata Gari Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

A cewar NDLEA, Nansubuga ta shiga Nijeriya ne ranar 29 ga watan Oktoba tare da wasu mambobin cocinta domin yin addu’o’i a cocin Synagogue Church of All Nations (SCOAN), da ke Lagos.

Hukumar ta ƙara da cewa sauran mambobin sun koma Uganda bayan gudanar da taron addu’o’i amma ita ta ci gaba da zama a Nijeriya inda ta karɓi koken a madadin ƙawarta mai suna Joy, wadda ke zaune Uganda.

NDLEA ta ce za a gurfanar da matar a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending