News
Wasu Bata Gari Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun kwance tare da sace fanka 25 a wani babban masallacin Kanzul Mudalsam da ke unguwar Gwammaja, a kan titin Katsina, cikin birnin Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na Ƙaramar Hukumar Dala, Sagiru Nazifi Yakasai, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.
Shugaban NUJ Na Ƙasa Ya Yi Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Abbas Ibrahim
Ya ruwaito wani mai taimaka wa ƙungiyar Gwammaja Inafita, Alhaji Salisu Sabon Titi, yana bayyana damuwarsa kan ƙaruwar satar kayayyaki da ayyukan daba a yankin.
Salisu ya ce ɓarayin na sace kayan masallaci da sauran kayayyaki masu daraja, ciki har da na’urorin hasken wuta, tare da lalata turakun da ake ɗora fitilun a kansu.
Ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta sa mazauna yankin fargaba, inda da dama suka daina zirga-zirga bayan ƙarfe 6 na yamma.
A cewarsa, an kuma sace babura biyar a makon da ya gabata, yayin da wasu mazauna yankin suka rasa wayoyinsu a hannun ɓarayi.
Salisu ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da rundunar haɗin gwiwar hukumomin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucinsu, ƙarƙashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado, da su gaggauta ɗaukar matakan magance matsalar tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
