Connect with us

News

Shugaban NUJ Na Ƙasa Ya Yi Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Abbas Ibrahim

Published

on

images (5)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida na Ƙasa (NUJ), Comrade Alhassan Yahya Abdullahi, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga tsohon shugaban NUJ na Jihar Kano, kuma ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party, Comrade Abbas Ibrahim, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Binta Ibrahim.

Hajiya Binta Ibrahim ta rasu ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2026, tana da shekaru 91, bayan fama da doguwar jinya.

Jami’an Yansanda Sun Kwato Shanu 39 Da Aka Sace Bayan Musayar Wuta Da Barayin Shanu A Kaduna

A saƙon ta’aziyyarsa, shugaban NUJ na ƙasar ya jajanta wa Comrade Abbas Ibrahim, sauran ’yan uwa da iyalan mamaciyar bisa wannan babban rashi.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar kura-kuranta, Ya jikanta da rahama, Ya kuma sanya ta cikin waɗanda za su shiga Aljannatul Firdaus.

Marigayiya Hajiya Binta Ibrahim ta bar ’ya’ya da dama, ciki har da Salamatu Saminu, wadda ta yi ritaya daga aikin gwamnatin Jihar Kano; Halima Ibrahim da kuma Comrade Abbas Ibrahim.

Advertisement

An gudanar da sallar jana’izarta a ranar Juma’a a Sahaba, Kundila, Kano, bayan kammala sallar Juma’a.

Allah Ya gafarta mata, Ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarta, Ya kuma ba iyalanta haƙurin jure wannan rashi. Amin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending