News
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
Cibiyar Wole Soyinka ta aikin jarida don binciken ƙwaƙwaf WSCIJ, ta zaɓi fitaccen mai ɗaukar hotunan labarai kuma ɗan jarida mai zaman kansa na kamfanin dillancin labarai na Associated Press, Sani Mohammed Maikatanga, a matsayin ɗaya daga cikin alƙalan kyautar Wole Soyinka ta Aikin Jarida na Bincike karo na 21.
Hakan na ƙunshe cikin wasiƙar gayyata da babbar daraktar cibiyar, Motunrayo Alaka, ta sanya wa hannu. A na karrama ƴan jarida a Najeriya da aikinsu ya nuna ƙwarewa a binciken labarai, jarumtar kare ƙa’idojin aikin jarida, ƙirƙire-ƙirƙire da jajircewa wajen hidima ga al’umma.
Saudiyya Za Ta Ci Gaba Da Rufe Filin Jirgin Saman Riyadh Saboda Hare-Haren Houthi
A matsayinsa na alƙali, Maikatanga zai haɗa kai da sauran alƙalan wajen tantance labaran da su ka tsallake matakin farko, da tantance waɗanda za su kai matakin ƙarshe da kuma zaɓen waɗanda su ka yi nasara a fannoni daban-daban.
Kyautar ta shekarar 2026 za ta ƙunshi fannoni shida da su ka haɗa da jaridun takarda, rediyo, talabijin, ɗaukar hotuna, aikin jarida ta intanet da zane-zanen sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Cibiyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewar Maikatanga za ta taimaka wajen tabbatar da adalci, gaskiya da sahihanci a tantance ayyukan da aka gabatar.
Maikatanga ya tabbatarwa da Matashiya TV cewa ya amince da tayin, inda ya bayyana shirinsa na bayar da gudummawa wajen tabbatar da adalci da rashin nuna son kai a zaɓen waɗanda za su lashe kyautar.
