Connect with us

News

Ahmad Hamisu Gwale Na Gidan Radiyon  Premier Ya lashe kyautar gwarzon mai karanta labarai na Najeriya

Published

on

FB IMG 1791896687376

Ahmad Hamisu Gwale na Premier Radio Kano, ya lashe kyautar Gwarzon Mai Karanta Labaran Rediyo na Maza a bikin bayar da kyaututtukan Nigerian Broadcasters Merit Awards (NBMA) karo na bakwai.

An bayyana sunansa cikin jerin waɗanda suka lashe kyaututtukan NBMA na shekarar 2026, a rukunin Radio and On-Air Personalities, inda ya samu lambar yabo ta Best Radio Newscaster (Male).

Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026

Wannan karramawa ta zo ne a matsayin wata alama ta amincewa da gudummawar da yake bayarwa a fannin watsa labarai, musamman wajen gabatar da labarai a rediyo.

Nigerian Broadcasters Merit Awards wani dandali ne da ke karrama ƙwararrun ma’aikatan rediyo da talabijin da kuma sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar yaɗa labarai ta Najeriya.

Nasarar Ahmad Hamisu Gwale ta ƙara sanya sunan Premier Radio cikin jerin gidajen rediyon da ma’aikatansu suka samu karramawa a wannan biki.

Advertisement

Wannan nasara ta zama abin farin ciki ga Premier Radio da sauran abokan aikinsa, tare da ƙarfafa gwiwar ƙwararrun yan jarida wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu na sanar da al’umma cikin ƙwarewa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending