News
INEC Ta Bayyana Dalilin Cire Wasu ’Yan Takarar Gwamna Daga Jerin Sunayen Da Ta Fitar
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa ta cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen waɗanda za su fafata a zaɓen 2027 saboda jam’iyyunsu sun gaza miƙa rajistar mambobinsu kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.
INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, inda ta ce ta ɗauki matakin ne bisa hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya tabbatar da cewa wajibi ne dukkan jam’iyyun siyasa su miƙa rajistar mambobinsu kafin gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani.
TSARIN KAURAN GWANDU: Yadda Malami Ke Doke Sauran Gwamnoni a Fadin Najeriya
Hukumar ta ce Kotun Ƙolin ta kuma tabbatar da cewa jam’iyyun da suka gaza bin wannan doka ba su cancanci tsayar da ’yan takara a zaɓen ba.
Sai dai INEC ta bayyana cewa jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa an riga an fitar da su tun ranar 12 ga Satumba, kwanaki 13 kafin hukuncin Kotun Ƙolin.
Sanarwar, wadda Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, ta ce jam’iyyun da ke ganin an cire sunayen ’yan takararsu bisa kuskure suna da damar sanar da hukumar cikin kwanaki 14.
INEC ta ce wa’adin sanar da ita game da irin wannan ƙorafi zai ƙare ne ranar 24 ga Oktoba, 2026, tare da jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya, bin doka da sahihancin zaɓe.
