News
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama wasu ’yan ƙasar biyu da ke zaune a Turai bisa zargin haɗiye ƙunshin hodar iblis guda 200 mai nauyin kilogiram 3.46, yayin da suke shirin tafiya daga Abuja zuwa Paris ta Faransa.
An kama mutanen ne ranar Laraba, 28 ga Oktoba, yayin binciken fasinjojin jirgin Air France mai lamba AF 832 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
An Kara Kudin Shiga Gidajen Kallon Kwallo A Kano
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi, ya ce binciken na’urar tantance jiki ya nuna cewa mutanen biyu sun haɗiye miyagun ƙwayoyin.
Sanarwar ta ce daga bisani sun fitar da dukkan ƙwayoyin da suka haɗiye yayin da jami’an hukumar ke sanya musu ido.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, wanda ke zaune a Faransa kuma yake aiki a masana’anta, ya isa Nijeriya ranar 21 ga Oktoba domin hutun ɗan lokaci.
Hukumar ta ce mutumin ya amsa cewa ya haɗiye ƙunshi 110 na hodar iblis, waɗanda suka yi nauyin kilogiram 1.901 bayan ya fitar da su.
Shi ma abokin tafiyarsa ya amsa haɗiye ƙunshi 90 na ƙwayar bayan binciken na’urar tantance jiki ya tabbatar da hakan. Ƙwayoyin da ya fitar sun yi nauyin kilogiram 1.559.
NDLEA ta ce kamen na daga cikin wasu samame da ta gudanar a sassa daban-daban na ƙasar, inda ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da dama, ciki har da tabar wiwi da wasu ƙwayoyi masu sarrafawa, tare da kama wasu mutane da ake zargi da safararsu.

